'Ba za a kammala titin Abuja zuwa Kano a zamanin Buhari ba' – BBC

Asalin hoton, BuhariSalau
Gwamnatin Najeriya ta ce sai nan da shekarar 2025 za a kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kano da aka fara a 2018.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a Kaduna, na wani babban ayari na gwamnatin tarayya.
"Nan da shekarar 2022 ne za a kammala hanyar da ke tsakanin Kaduna da Zaria, wanda wannan babban ci gaba ne.
"A 2023 za a kammala hanayar da ta tashi daga Kaduna ta dangane ga Kano, sai kuma a 2025 za a kammala hanyar Abuja zuwa Kano baki ɗayanta," in ji Fashola.
Tawagar gwamnatin tarayyar ta ziyarci aikin da ake yi tsakanin Kaduna zuwa Kano inda ta ce ta gamsu da yadda ake gudanar da aikin, duk kuwa da cewa wasu al'ummar ƙasar na ƙorafi kan yadda wannan aiki ke tafiyar hawainiya.
Cikin tawagar har da shugaban ma'aikatan shugaban kasa Ibrahim Gambari, wanda ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce "mun gamsu da ingancin aikin a wuraren da aka kammala, duk da cewa akwai 'yan matsaloli."
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, na cikin tawagar sai dai ra'ayinsa ya sha bamban da na ministan ayyukan, in da ya ce " za'a kammala aikin cikin wannan lokaci da shugaba Buhari ke jagorantar Najeriya."
Wani Abu da masu bin hanyar ke ƙorafi a kai shi ne rashin tabbas da duk wani mai bin hanyar ke fuskanta har sai ya ga ya isa inda ya nufa.
Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW na jihar Kaduna Alhaji Bature Yusuf Sulaiman, ya ce abin takaici ne yadda ake jan ƙafa a wannan aiki.
"Duka direbobinmu na cikin matsala sakamakon ɗaukar lokaci da wannan hanya ta yi, a wasu lokutan sai dai direba ya yi hakuri ya zaɓi rami mai gwara-gwara ya faɗa amma akwai inda ba ka isa ka wuce ba sai ka shiga rami.
"Matsala ta biyu ita ce ɓarayi na amfani da damar nan suna kama mutane su yi garkuwa da su abu ne da ke faruwa kusan ko wacce rana, wannan ya sanya mutane cikin wata damuwar ta daban," in ji Alhaji Bature.
Ko a ƙarshen makon da ya gabata sai da masu garkuwa da mutane suka tare hanyar tare da kama mutane da dama, baya ga harbin motar mutane da suke yi idan suka ƙi tsaywa.
A 2018 ne aka kaddamar da wannan aiki da zimmar ba shi taƙaitaccen lokaci da za a kammala shi, amma duka a ƙarƙashin shugabancin Muhammadu Buhari.
Asalin hoton, NIGERIA GOVT
Gwamnatin Najeriya ta ware kuɗi fiye da naira biliyan 155 domin aiwatar da aikin gyaran hanyar mai nisan kilomita fiye da 400.
A 2017 ne gwamnatin kasar ta amince da aikin bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka yi karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.
Hanyar dai ta dade da lalacewa, al'amarin da kan janyo haɗuran motoci a waɗansu lokuta tare da asarar rayuka.
A shekarar 2017 ne gwamnatin kasar ta gyara wani bangare na hanyar wato tsakanin Abuja zuwa Kaduna lokacin da aka rufe filin jirgin saman Abuja domin hanyar jirgi da za a gyara.
Sai dai daga bisani hanyar ta kara koma gidan jiya.
A lokacin da aka ƙaddamar da wannan aiki, Ministan lantarki da ayyuka da kuma gidaje na Najeriya Babatunde Fashola ya ce an ware kuɗaɗe da suka kai naira biliyan 155 domin aiwatar da aikin.
Sai ga shi a watan mayun 2020, Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya ce gwamnati ta karɓi sama da dala miliyan 311 daga Amurka daga cikin kudaden da ake zargin tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha ya sace.
Malami ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen wajen kammala ayyuka a sassan Najeriya da suka haɗa da hanyar Legas zuwa Ibadan da hanyar Abuja zuwa Kano da kuma gadar Neja.
A gefe ɗaya kuma wasu kafafen yaɗa labaran ƙasar na cewa, ba a bai wa kamfanin da yake aikin kuɗinsa ba ne baki ɗaya, kamar yadda aka saba yi a yarjejeniyar kwangila.
Wannan dalilin ya sanya ita ma gwamnatin tarayya ba ta matsawa kamfanin kan sai ya kammala aikin ba.
Ina naira miliyan 155 da aka ware a 2018, ina kuma kuɗaɗen da aka karɓo daga Amurka da ake zargin Abacha a wawure? wannnan ce tambayar da mafi yawan 'yan ƙasar ke yi.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds