Ana cigaba da yaɗa iƙirari daban-daban a shafukan sada zumunta yayin da ake yin zanga-zangar ƙin jinin tsare-tsaren gwamnati a Najeriya.
Masu zanga-zangar dai na kokawa ne akasari game da tsada da kuma wahalar rayuwa a faɗin ƙasar.
An shirya ta ne akasari a shafukan sada zumunta, inda masu tsara ta suka ci alwashin ɗaukar kwana 10 suna gudanar da ita har sai gwamnati ta biya musu buƙatunsu.
Sai dai da alama masu zanga-zangar da ma ɓangaren gwamnati duka sun yaɗa labaran ƙarya domin kafa hujja kan junansu.
Akwai hotunan da aka ce na 2011 ne, da kuma yadda aka nuna cewa Peter Obi ya jagoranci zanga-zangar a Abuja ranar Alhamis.
Ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya wallafa a shafinsa na X yana zargin gwamnatin ƙasar da "ɓata wa 'yanƙasar suna".
Ya yi iƙirarin cewa wasu hotuna da aka yaɗa tsofaffi ne tun na 2011.
Ya wallafa hoton wani saƙo a Facebook da kakakin ‘yansandan Kano ya wallafa ɗauke da hotunan wasu da ake zargi da satar kayan jama’a, inda ya ce tsofaffi ne daga 2011.
Sai dai tawagar binciken gaskiya ta BBC ta gano cewa iƙirarin nasa ba gaskiya ba ne, kuma hotunan da kakakin ‘yansandan Abdullahi Haruna Kiyawa ya saka na wannan zanga-zangar ce.
Kiyawa ya wallafa hotuna da dama na mutanen da aka kama da zargin, waɗanda Mista Sowore ya ce tun a 2011 kakakin ya wallafa da kansa.
Sai dai babu wannan saƙon a shafin Kiyawa na Facebook a 2011.
Bugu da ƙari, bincikenmu ya nuna kayayyakin da aka sata sun yi daidai da irin waɗanda aka gani a hotunan da wakilin BBC hya ɗauka a Kanon.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Babu karin bayanai
Haka nan, Kiyawa ya fito a ɗaya daga cikin hotunan tare da wasu da aka kama, kamar yadda Sowore ya wallafa, sai dai kuma har sai a 2019 ya zama kakakin 'yansandan.
Kazalika, kakin da Kiyawa ke sanye da shi sai a 2012 'yansandan Najeriya suka fara amfani da su.
Hakan na nufin ba zai yiwu a ɗauki hotunan ba a lokacin.
Asalin hoton, NG Police
Ita ma rundunar 'yansandan ta Kano ta fitar da sanarwa tana musanta iƙirarin na Sowore a shafinta na Facebook.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Facebook
Babu karin bayanai
Wani labarin na ƙarya da aka yaɗa shi ne cewa tsohon ɗantakarar jam'iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa ya jagoranci wani ayari na masu zanga-zangar a Abuja.
Tawagarmu ba ta samu wata hujja ba da ke tabbatar da cewa Obi ya ɗauki nauyin zanga-zangar.
BBC ta gano wani bidiyo da aka wallafa ranar 25 ga watan Yunin 2024, wanda ke goyon bayan Santa Ireti Kingibe da aka gan su tare a bidiyon.
Duka 'yansiyasar biyu sun musanta zargin cewa wajen zanga-zangar da ake yi ce yanzu.
Mista Obi ya ce an dauki bidiyon ne a lokacin da ya kai ziyara hedikwatar jam’iyyar Labour, inda ya sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin jam’iyyar da ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC).
"An haɗa bidiyon ne don ƙirƙirar labari na ƙarya, kuma tabbas an biya waɗanda ke yaɗa wannan ƙirƙiraren labarin. Irin wannan rashin gaskiya ba shi da mazauni a dimokradiyyarmu, inda ya kamata a ce an tabbatar da gaskiya da riƙon amana," in ji shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Babu karin bayanai
Duk da cewa Obi ya goyi bayan 'yancin mutane na zanga-zanga, babu wata hujja da ke nuna cewa ya ɗauki nauyi ko kuma shirya ta.
Sai dai kuma, wasu daga cikin magoya bayansa na cikin masu goyon bayan zanga-zangar sosai.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Labaran ƙarya da aka yaɗa kan zanga-zangar matsin rayuwa a Najeriya – BBC
