Asalin hoton, Getty Images
Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Abuja babban birnin Najeriya ya amince da hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta rinƙa gudanar da gwajin ƙwayoyi ga waɗanda za su yi aure.
Shugaban majalisa, Sarkin Abaji, wato Ona na Abaji, Alhaji Adamu Yunusa, shi ne ya bayar da wannan umarni tare da kira a soma aiwatar da wannan tsari nan take.
Wannan tsarin zai tabbatar da cewa dole masu son yin aure su gabatar da shaidar gwajin ƙwayoyi kafin a ɗaura musu aure.
Tun a watan Oktoba na 2021 ne hukumar NDLEA ta kawo shawarar gudanar da wannan gwaji na tilas.
Shugaban hukumra, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya bayyana cewa tilasta wa masu son yin aure yin wannan gwajin zai rage yadda mutane ke ta'ammali da ƙwayoyi a ƙasar.
Ona na Abaji ya jaddada cewa ta'ammali da miyagun ƙwayoyi matsala ce babba ga Najeriya inda matsalar ta shafi matasa maza da mata.
Daga ciki har da ma'aurata waɗanda ya kamata a ce suna jin daɗin aurensu.
A yayin tattaunawa da sarakunan gargajiya na Abuja, Buba Marwa ya bayyana cewa adadin matsalolin da ake samu na matan da mazansu ke dukansu ya ƙaru kuma adadin na ƙaruwa ne sakamakon ƙwayoyin da mazan ke sha a lokuta da dama.
Ya bayyana cewa akwai buƙatar Najeriya ta karbi wannan tsarin na gwajin ƙwayoyi ga masu son yin aure kamar yadda ake na cuta mai karya garkuwar jiki da sauran cutuka.
NDLEA ta bayyana cewa ko da ɗaya daga cikin ma'auratan an yi gwajin an tabbatar da yana ta'ammali ko macen tana yi, za a iya kai su asibiti kafin auren domin duba lafiya don guje wa faruwar wani mummunan abu.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Za a soma yi wa waɗanda za su yi aure gwajin miyagun ƙwayoyi a Abuja – BBC
