Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun yi awon gaba da Sarkin garin Rubochi da ke karkashin karamar hukumar Kuje ta Abuja.
An dai ce 'yan bindigar sun je gidan Etsu Mohammed Ibrahim Pada ne da misalin karfe biyu na daren Talata, inda suka yi amfani da bindiga wajen fitar da basaraken daga dakinsa sannan suka yi awon gaba da shi.
Wata 'ya ga Sarkin na Rubochi ta shaida wa BBC cewa "ba a samu rasa rai ba amma kuma 'ya'yan sarkin guda biyu sun jikkata sakamakon tunkarar dakin mahaifin nasu da suka yi bayan sun jin hatsaniya".
"Y'ayan sarkin na barci a bangarensu sai suka ji hatsaniya inda suka ruga domin ceton baban nasu amma da zuwansu sai maharan suka hau su da sara da adda."
Ta kara da cewa 'yan bindigar sun kwace wayarta da ta mahaifiyarta sannan suka yi awon gaba da abubuwa da dama da suka hada da kayan abinci.
Al'amarin dai ya jefa al'ummar garin cikin rudani sakamakon harbin kan-mai-uwa-da-wabi da maharan suka yi ta yi.
Wasu rahotanni na cewa tuni aka fara magana da masu garkuwar domin tattauna yadda za a kubutar da basaraken, sai dai 'yar sarkin da muka zanta da ita ta ce ba ta da masaniya.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Yadda 'yan bindiga suka yi garkuwa da basarake a Abuja – BBC
