Abuja-Kaduna: Yadda matafiya suka shiga tasku – BBC

Matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sun shiga tasku a ranar Juma'a bayan da hanya ta cushe sakamakon tare hanya da direbobin manyan motoci suka yi.
Rahotanni sun ce direbobin sun nuna fushinsu ne game da kashe abokin aikinsu da wani dan sanda ya yi da farar safiyar Juma'a.
Rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna ta yi Allah-wadai da lamarin, inda tace za a ladabtar da 'dan sandan da ake zargi ya yi harbin.
Wakiliyar BBC Madina Dahiru Maishanu wacce lamarin ya rutsa da ita ta ce mutane sun galabaita har ma suka rika neman a taimaka masu da ruwa da abinci wadanda suka yanke a wurin baki daya.
Ta ce wasu matafiyan sun ringa bi motoci suna rokon a taimaka musu da burodi saboda tsananin yunwa.
Wasu matafiya sun kama yin wasu abubuwa da za su debe musu kewa, yayin da suka yi dogon jiran a bude hanya domin ci gaba da tafiyoyinsu.
Abin ba iya mutane ya shafa ba domin kuwa har da dabbobi da tsintsaye suma sun shiga mawuyancin hali.
Madina Maishanu ta ce wasu 'yan tsaki da dama sun mutu saboda zafi, abinda ya sa wadanda ke tafiya da su a mota suka fito da sauran waje domin shan iska.
Mutane da dama sun bayyana bacin ransu a shafukan sada zumunta tare da kiraye-kirayen da a kawo masu dauki.
Wasu ma gwamna Nasir El-rufai suka kira kai-tsaye domin samun dauki. Wannan kira ya yi ga gwamnan da ya tallafa masu domin kuwa direbobin sun ce kowa ya yi zaman dabaro a titi:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Babu karin bayanai
Shi kuwa gwamnan sai ya mayar da martani da cewa hakan "abin takaici ne kuma ina kan hanyar zuwa wurin da kaina, kuma za mu kama tare da gurfananr da su a gaban kotu".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Babu karin bayanai
Shi kuwa wannan cewa ya yi sun shafe sa'o'i uku a cikin cunkoson da ya ki gaba ya ki baya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Babu karin bayanai
Daga baya ne kuma kwamishinan harkokinn cikin gidan jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ya ce an bude hanyar:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Babu karin bayanai
Sai dai har bayan ya wallafa wancan bayani mutane na ci gaba da kokawa kan halin da suke ciki.
Rundunar 'yan sanda ta kaduna ta fitar da sanarwa, inda ta ce tuni kwamishinan 'yan sanda Ali A. Janga ya umarci da a tube dan sandan da ake zargi daga aikinsa sannan kuma a yi bincike.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds