Gwamnonin APC, ministoci da shugabannin jam'iyya sun gana da dare a Abuja – Legit.ng

Global site navigation
Na gargajiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja – Gwamnonin da suka ɗare kan mulki karƙashin inuwar jam’iyyar APC sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa a daren Laraba a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin da wasu ministoci sun yi ganawar sirri a gidan gwamnan jihar Imo da ke unguwar Asokoro a birnin tarayya Abuja.


Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa taron ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da wasu ministoci da masu mukamai a gwamnati mai ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika ƴan kwamitin gudanarwa na ƙasa watau NWC na APC wanda Ganduje ke jagoranta sun halarci taron.
Cikin ministocin da suka halarta akwai, Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya (AGF), Lateef Fagbemi (SAN), da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo (SAN)
Sauran sun haɗa da Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Mohammed Maigari Dingyadi da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama'a, Mohammed Idris.
Bayanai sun nuna cewa kusan gwamnoni 20 na jam’iyyar APC ne suka halarci taron, wanda aka yi a siirince jiya Laraba, 14 ga watan Mayu, 2025.
Wannan taro na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC ke ƙara ƙarfi sakamakon yadda ƴan siyasa da shugabanni ke tururuwar sauya sheka zuwa cikinta.


Idan baku manta ba gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, magabacinsa kuma abokin takarar Atiku a 2023, Ifeanyi Okowa da duka ƴan majalisa da shugabannin PDP a jihar sun koma APC
A wannan makon da muke ciki, sanatocin PDP uku daga jihar Kebbi suka sanar da sauya sheƙarsu zuwa APC a hukumance a zaman Majalisar Dattawa.
Sanatocin sune, Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya), Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa), da Garba Maidoki (Kebbi ta Kudu).
Har yanzu ba a bayyana cikakken dalilin ganawar gwamnonin APC da ministocin ba, amma ana kyautata zaton yana da alaka da harkokin jam’iyya da cigaban siyasa a kasa.
Sannan ana ganin taron zai maida hankali kan haɗin kan shugabanni da masu mulki da kuma lalubo hanyar kara ɗaga APC gabanin zaɓe na gaba a 2027.
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban APC na ƙasa kuma sanatan Edo ta Tsakiya, Adams Oshiomhole ya ce ko yau aka ajiye akwatun zaɓe Tinubu zai samu nasara.


Sanata Oshiomhole, tsohon gwamnan Edo ya ce nasarorin da Bola Tinubu ya samu daga hawa mulki zuwa yanzu, ya ƙara masa masoya a tsakanin ƴan Najeriya.
Ya ce shugaban ƙasa ya karɓi mulki a lokacin da tattalin arzikin ƙasa ke tsaka mai wuya, amma yana iya baki ƙoƙarinsa wajen saita al'amura.
Asali: Legit.ng
Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma’aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al’amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262





Duba karin labarai a nan

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds