Asalin hoton, Nyesom Wike/Twitter
Ministan birnin tarayyar Najeriya, Nyesom Wike, ya amince da ƙwace filayen wasu ɗaiɗaikun mutane a unguwar masu kuɗi ta Maitama da ke Abuja saboda rashin sabunta takardun mallakar filaye na tsawon shekaru.
Cikin jerin sunayen da sashen BBC Pidgin ya gani akwai fili mallakin gidauniyar tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda aka ce ana bin su bashin sama da naira biliyan daya.
"Bayan cikar wa'adin alfarma da ministan Abuja ya bayar ga masu filayen domin su biya kudaden da ake bin su bashi, hukumar birnin tarayya Abuja ta ƙwace izinin mallakar filayen nasu," in ji wata sanarwa da hukumar FCTA ta fitar.
A cewar sanarwar, hakan na kan tsarin dokar mallakar filaye ta 1978 ta Najeriya, wadda ta ce gwamnatin na da ikon ƙwace fili idan wanda yake da shi ya kasa cika sharuddan da doka ta tanada.
Umarnin ya shafi manyan mutane da dama, ciki har da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, da matarsa Regina, wadanda ake bin bashin sama da miliyan 34 na kudin sabunta shaidar mallakar filayen.
Akwai manyan ƴan siyasa da suka hada da Sanata Dino Melaye, wanda ya yi takarar gwamnan jihar kogi, da Sanata Shehu Sani dan fafutuka da ya yi takarar gwamnan Kaduna, da tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okoracha, da Sanata Abdul Ningi, da tsohon alƙalin alƙalan Najeriya Walter Onnoghen, da Sanata Enyinnaya Abaribe daga jihar Abia.
Lamarin ya shafi har da cibiyoyin addini kamar cocin Methodist Church ta Nigeria da ake bi bashin kusan miliyan biyu.
Bayan ƙwace filaye kusan 762 da FCTA ta yi, akwai kuma jerin sunayen wadanda suka biya wani kaso na abin da ake bin su bashin, inda hukumar ta yi kira da su gaggauta kammala biyan kudaden da suka rage cikin mako biyu.
Babu cikakken bayanin da ke nuna tsawon shekarun da mutanen suka kwashe ana bin su bashin, kuma babu bayanin kudin da ya kamata su biya duk shekara.
Haka nan, babu cikken bayanin da ke nuna ko matakin shi ne na ƙarshe ko kuma za su iya daukar wani matakin daban kafin ƙwace filayen.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin sashen watsa labarai na FCTA domin jin ƙarin bayani, sai dai har zuwa lokacin da haɗa wannan rahoton ba a samu amsa daga garesu ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Nyesom Wike yake ƙwace filayen manyan mutane a Abuja ba tun bayan da ya zama ministan binrin.
A watan Satumbar 2023, ya ƙwace filayen manyan ƴan siyasa da alƙalai da kamfanoni da kuma ɗaiɗaikun mutane, ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar a jam'iyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi.
Dalilin da ya bayar na ƙwace filayen a wancan lokacin shi ne rashin gini a kan lokacin da gwamnati ta bayar.
Sashen kula da filaye na hukumar birnin tarayya Abuja wato FCTA shi ne ke kula da mallakar filaye a birnin.
A cewar sashen, ma'aikatar ce ke da alhakin kula da dukkan filayen da ke birnin a bisa dokokin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Doka ta yi tanadin cewa gwamnan jiha ko ministan Abuja, su ne ke da ikon kula da filaye na jiharsa, amma ban da filayen da gwamnatin tarayya ta mallaka ko kuma wani wakilinta.
Kuma su ne yake da alhakin bayar da izinin mallakar filayen gina gidaje da na kasuwanci da na noma da dukkan sauran ɓangarori.
A cewar hukumar ta FCTA, duk wanda ke son mallakar fili zai nemi izini ne daga wajen sashen kula da filaye na hukumar, domin su ne ke da ikon bayar da izinin mallakar filaye, kuma su ne suke da ikon ƙarbar dukkan harajin filaye.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Wike ya ƙwace filayen Gidauniyar Buhari da wasu manyan ƴansiyasa a Abuja – BBC
