Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai tsaye – 23/10/2024
Muhammad Annur Muhammad
Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafi da muka kawo labaran abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya. Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.
A madadin ni Isiyaku Muhammed da sauran abokan aiki nake cewa mu kwana lafiya.
Asalin hoton, Sulaiman Bala Idris
Gwamnonin jihohin Zamfara da Katsina Dauda Lawal da Dikko Radda sun yi wata ganawar sirri da ministan tsaro, Badaru Abubakar da kuma mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a Abuja.
Zamfara State Governor Dauda Lawal and Katsina State Governor Dikko Radda held a closed-door meeting with Defence Minister Badaru Abubakar and National Security Adviser Mallam Nuhu Ribadu.
Ganawar da aka yi tun jiya Talata, bayanai na nuna cewa ta mayar da hankali ne kan samar da hanyoyin da za su haɗa ƙarfi da ƙarfe tar da duba sabbin hanyoyin da za a bi domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankunansu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Zamfara Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce gwamnonin sun tattauna wa ministan da mai ba shugaban ƙasar shawara ne a kan wasu shawarwari da haɗakar ƙungiyoyin arewa wato CNG suka gabatar domin samar da zaman lafiya a jihohinsu, da sauran abubuwan da suka shafi tsaro.
Taron ya kuma samu halartar shugaban kwamitin amintattu na NCG, Alhaji Nastura Ashir Shariff da sauran mambobin kwamitin tsaro na ƙungiyar.
Asalin hoton, Getty Images/AFP
Bankin lamuni na duniya IMF ya ce kuɗin Najeriya ya fara nuna alamar farfaɗowa a wannan shekarar ta 2024.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto da IMF ɗin ya fitar a birnin Washington DC, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A cewar IMF, "Rage nauyin kuɗaɗen waje da babban bankin Najeriya ya yi, da ƙara kuɗaɗen ruwa sun taimaka wajen fara farfaɗo da kuɗin ƙasar."
Tobias Adrian, daraktan harkokin kuɗaɗe da hannun jarin kasuwanni ya bayyana cewa ƙoƙarin bankin CBN ne ya kawo wannan nasarar.
A karon farko matar nan da aka yi wa fyaɗe sau da dama wadda labarinta ya girgiza mutanen Faransa ta bayyana a gaban kotu.
Tsohon mijin Jisel Pe-li-kot ya amsa cewa yana gayyato gomman maza suna kwanciya da ita bayan ya gusar mata da hankali.
Ta shaida wa kotu cewa waɗanda aka yi wa fyaɗe bai kamata su ji kunya ba, waɗanda yi aikata laifin ne suka aikata abun kunya.
Wakilin BBC ya ce Jisel Pelicot ta ce ta tsaya gaban kotun ne saboda waɗanda aka yi wa fyaɗe nan gaba su samu ƙwarin gwiwar bayyana yadda aka ci zarafinsu.
Yawancin waɗanda suka aikata fyaden sun bayyana cewa ba su san matar ƴar shekara 72 ba ta cikin hayyacinta a lokacin.
Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu wasu masu binciken Amurka suna mamaki tare da fara binciken yadda wasu muhimman bayanan sirrin Amurka suka yaɗu a kafafen sadarwa.
Takardun, waɗanda suka bayyana a kafar Telegram a ranar Juma'a, sun ƙunshi wasu bayanai na sirri da ake tunanin bayanan nazari ne da Amurka ta yi a kan shirye-shiryen Iran na mayar da martanin a Iran.
A ranar Litinin, kakakin hukumar tsaro na fadar shugaban ƙasar Amurka, John Kirby ya ce shugaban ƙasa Joe Biden ya shiga damuwa sosai a game da yadda bayanan suka fita.
Har yanzu jami'an gwamnati ba sun kasa gane yadda takardun suka fita, inda suke ta tantamar ko dai an musu kutse ne, ko kuma satar su aka yi, aka fitar da su, in ji Mista Kirby.
Wasu makonni da suka gabata ne Isra'ila na bayyana ƙudurinta na ƙaddamar da hari a Iran a matsayin martani ga hare-hare Iran ɗin a Isra'ila a ranar 1 ga Oktoba.
A ɓangaren ta Iran ɗin, ta ce ta kai hare-haren ne bayan Isra'ila ta kashe shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah a ranar 27 ga Satumba.
>>>>Cigaban labarin>>>>>
Ministan aikace-aikacen Najeriya, David Umahi ya ba kamfanin Julius Berger wa'adin mako ɗaya ya amince da naira biliyan 740.79 domin ƙarasa kilomita 82 na ɓangare na biyu na titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano.
Umahi ya bayyana hakan ne a lokacin da sabon manajan darakta na Julius Berger Plc, Dr Pier Lubasch ya kai ziyara ma'aikatar ayyuka tare da rakiyar tsohon manajan daraktan, Dr Dr Lars Richter a Abuja.
A wata sanarwa da mai ba ministan shawara a kan harkokin watsa labarai, Orji Uchenna ya fitar a ranar Laraba, ya ce idan kamfanin bai amince da kwantiragin ba, za a iya ƙwace aikin.
"Ministan ayyauka Sanata Nweze David Umahi, ya buƙaci kamfanin Julius Berger ya amince da sabuwar yarjejeniyar aikin ƙarasa aikin na ɓangare na biyu na titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano a kan kuɗi naira biliyan 740, 797,204,713.25," in ji shi, inda ya ƙara da cewa rashin ƙarasa aikin ya jefa mafiya cikin ƙunci.
"Don haka idan Berger ba za su yi aikin ba, sai mu nemi kamfanin da zai ƙarasa aikin. Kuɗin kwangilar ya tashi daga naira biliyan 710 zuwa biliyan 740 saboda jan ƙafa da kamfanin ke yi, kuma idan aka ci gaba a haka, kuɗin zai ƙaru ne, wanda zai zama matsala ga ma'aikatar," kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
A ƙarshe, sanarwar ta ce ministan ya ba kamfanin wa'adin mako ɗaya ko dai ya amince da kwangilar, ko kuma idan bai amince ba, a ƙwace aikin.
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta yi gargadin cewa za ta dauki dakarun Koriya ta Arewa a matsayin halastattun waɗanda za a iya farmaki idan har suka yi yaƙi tare da dakarun Rasha a Ukraine.
Washinton ta ce aƙalla sojojin Koriya ta Arewa dubu uku ne aka tura Rasha domin ba su horo.
Sai dai mai magana da yawun fadar White House John Kirby ya ce babu tabbacin ko za a tura dakarun fagen daga.
Rasha da Koriya ta Arewa sun sha musanta zargin.
Gwamnatin Turkiyya ta ce mutum hudu sun rasu sakamakon harin ta'addanci da aka kai kan kamfanin sufurin jiragen sama, mallakin gwamnatin ƙasar, da ke kusa da babban birnin Ankara.
Wakiliyar BBC ta ce an samu rahotannin harbe-harben bindiga da ƙarar fashe-fashe.
Ministan harkokin cikin gida na Ali Yerlikaya ya ce an kashe mutum biyu mace da namiji da suka kai harin, kuma akwai yiuwar mambobin ƙungiyar ƴan awaren PKK ne.
Wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu mutum biyu suka fita daga mota dauke da makamai kafin daga bisani suka bude wuta.
Al`umma na cigaba da bayyana ra`ayoyinsu bayan an sanar wani hukunci da alƙalan kotuna a ƙasar Ghana da cewa an haramta hukunta laifin yunƙurin kashe kai a ƙasar, inda alƙalan suka ce daga yanzu ba laifi ba ne.
A wata takarda mai ɗauke da sa hannun mai shari’a Cyra Pamela Koranteng, Sakataren Shari’a, ta sanar da cewa alƙalai da kotun sun yi garambawul ɗin ne a kan dokar hukunta waɗanda suka tsallake rijiya da baya, bayan sun yi yunƙurin kashe kansu.
Asalin hoton, Khalifa Muhammad Sanusi ll fans
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai naɗa ɗansa na farko a matsayin Ciroman Kano.
Mahaifin Muhammad Sanusi II, Ambasada Aminu Sanusi ya taɓa riƙe sarautar, sannan Alhaji Nasiru Ado Bayero ya riƙe sarautar har zuwa lokacin da aka naɗa shi Sarkin Bichi a shekarar 2020.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa za a naɗa Aminu Muhammadu Sanusi, wanda ɗansanda ne tare da wasu mutum tara a ranar Juma'a, 25 ga Oktoban 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sauran waɗanda za a naɗa su ne Mahmud Aminu Yusufu a matsayin sabon Mai Unguwar Mundubawa; Dr. Abubakar Sanusi Usman Shehu II as Ɗan Galadiman Kano da Alhaji Abubakar Aminu Sanusi (Wambai) a matsayin Ɗan Madami.
Sauran su ne Arch. Ali Muktar a matsayin Sa’in Kano da Sarki Yusuf Bayero a matsayin Ƴan Daka da Abdullahi Idris Bayero a matsayin Fagacin Kano da Ado Abdullahi Aminu a matsayin Kaigaman Kano da Idris Sanusi a matsayin Sarkin Sulluɓawa da Mansur Isa Bayero a matsayin Sarkin Kudu sai Abdullahi Sarki Mohammed a matsayin Sarkin Yamma.
Asalin hoton, Reuters
Hezbollah ta tabbatar da cewa malamin da ake tunanin zai maye gurbin Hassan Nasrallah ya rasu a wani harin Isra'ila kimanin mako uku da suka gabata.
A jiya Talata ne rundunar sojin Isra'ila ta sanar da kashe malamin mai suna Hashem Safieddine a wani hari da ta kai a wajen Beirut.
A wata sanarwa da Hezbollah ta fitar, ta ce ƙungiyar na jimamin "shahidi kuma jagora na gari" wanda ya yi rayuwa mai kyau.
Safieddine ɗanuwan tsohon shugaban ƙungiyar Hassan Nasrallah wanda Isra'ila ta kashe a Lebanon a 27 ga Satumba.
Bayan rasuwarsa, Saffiedine ya fara jagorantar harkokin ƙungiyar, inda ake tunanin za a sanar da shi a matsayin sabon sakatare-janar na ƙungiyar, duk da cewa ba a kai ga sanarwar da shi ba a hukumance.
Bayanai sun fara fitowa a game da harin da aka kai a kamfanin sufurin jiragen sama, mallakin gwamnatin ƙasar Turkiyya.
Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya ya tabbatar da cewa mutum uku sun rasu, sannan wasu 14 sun jikkata.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X Ali Yerlikaya ya ce an kashe mutum biyu daga cikin waɗanda ake zargi da kitsa harin.
Asalin hoton, Pastor Umo Eno/Facebook
Gwamnan jihar Akwa Ibom Umo Eno ya sanar da fara biyan ma'aikatan jihar naira 80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi,
Gwamnatin jihar ta kuma kafa kwamitin tabbatar da tsarawa tare da tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin, inda gwamnan ya ba su wata ɗaya su kammala aikinsu.
Ini Ememobong, kwamishinan watsa labarai na jihar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce wannan matakin na cikin burin gwamnan ta inganta rayuwar ma'aikatan jihar da jin daɗinsu.
Asalin hoton, Tinubu/Facebook
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami ministoci biyar tare da naɗa wasu sababbi bakwai da kuma sauya wa goma ma'aikatu.
Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a shafinta na X, ta nuna cewa ministocin da aka cire su ne;
Waɗanda aka sallama:
1-Barr. Uju-Ken Ohanenye; ma'aikatar harkokin mata
2- Lola Ade-John; ministan harkokin yawon buɗe idanu
3- Farfesa Tahir Mamman; ministan ilimi
4- Abdullahi Muhammad Gwarzo; ƙaramin ministan gidaje da raya birane
5- Dr. Jamila Bio Ibrahim; ministar matasa
Waɗanda aka sauya wa ma'aikatu:
1-Hon Dr. Yusuf Tanko Sununu; ƙaramin ministan ilimi ya koma ƙaramin ministan jinƙai da rage talauci
2- Dr. Morufu Olatunji Alausa; ƙaramin ministan lafiya, ya koma ministan ilimi
3- Barr. Bello Muhammad Goronyo, ƙaramin ministan ruwa da tsafta, ya zama ƙaramin ministan ayyuka
4-Hon. Abubakar Eshiokpekha Momoh, ministan raya Naija Delta, ya koma ma'aikatar raya yankuna (sabuwa)
5- Uba Maigari Ahmadu, ƙaramin ministan ƙarafa ya koma ƙaramin ministan raya yankuna
6- Dr. Doris Uzoka-Anite, ministar masana'antu da kasuwanci da zuba jari ta koma ƙaramar ministar kuɗi
7- Sen. John Owan Enoh, ministan raya wasanni ya koma ƙaramin ministan kasuwanci da zuba jari (masana'antu)
8- Imaan Sulaiman-Ibrahim, ƙaramar ministar harkokin 'yansanda ta koma ministar mata
9- Ayodele Olawande, ƙaramin ministan matasa ya koma ministan raya matasa
10-. Dr. Salako Iziaq Adekunle Adeboye, ƙaramin ministan muhalli, ya koma ƙaramin ministan lafiya
Sababbin ministocin da aka naɗa;
Asalin hoton, Facebook/Nasiru Idris
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya sanya hannu a kan sabuwar dokar tsarin albashi mafi ƙanƙanta – naira 75,000, ga ma'aikatan jihar.
A lokacin bikin sanya hannu a kan dokar, da aka yi yau Laraba a fadar gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, gwamnan yaa jaddada ƙudurinsa da kare muradun ma'aikata da kuma tabbatar da jin daɗinsu.
Ya yi alƙawarin cewa ba zai taɓa barin ma'aikatan jihar su kunyata ba, inda ya ce sun kafa tarihi, kasancewar ya sanya hannu a kan dokar ne a ranar da majalisar gudanarwar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta NLC ke gudanar da taronta a jihar, inda shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ya kasance a wurin.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Gwamnan ya taka muhimmiyar rawa wajen batun aiwatar da sabon tsarin albashin mafi ƙanƙanta a Najeriya.
Ta ce a lokacin da yawancin gwamnoni ke cewa ba za su iya biyan sabon albashin ba, shi kuwa ya yi tsayin daka kan cewa gwamnoni za su iya.
Mutane da dama sun mutu wasu kuma sun ji raunuka sakamakon wata fashewa a wajen wani kamfanin ƙera kayan sararin samaniya a kusa da Ankara babban birnin Turkiyya.
Wata kafar yaɗa ta ƙasar ta ce an samu fashewa da kuma harbe-harbe a wajen kamfani Turkishi Aerospace Industries (TAI) mai nisan kilomita 40 daga cikin birnin.
Ministan Harkokin Waje Ali Yerlikaya ya wallafa a dandalin X cewa "an kai harin ta'addanci" kan kamfanin kuma "abin takaici an kashe wasu tare da jikkata wasu".
Za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu.
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci kwamitinta da ke kula da harkokin wutar lantarki ya gudanar da bincike kan matsalar yawan lalacewar layin samar da lantarki na ƙasar, ya kuma bayar da rahoto cikin mako uku.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, matakin ya biyo bayan amincewa da buƙatar da ɗan majalisar Mansur Mano Soro, daga jihar Bauchi ya gabatar a zamanta na yau Laraba.
Ɗan majalisar ya bayyana damuwa kan matsalar lalacewar layin lantarkin na ƙasa da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a kwanakin nan, lamarin da ke jefa ƙasar cikin rashin wuta tare da jefa 'yan ƙasar cikin matsin rayuwa da suke fama da shi.
Ya ce, wutar lantarki aba ce da ta zama wajibi wajen bunƙasar tattalin arziƙi da kuma cigaban duk wata ƙasa.
Hon. Mansur ya nuna takaicinsa yadda aka samu matsalar lalacewar layin wutar na ƙasa sau takwas a cikin wannan shekara ta 2024 kaɗai, inda ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa da takaici.
Ɗan majalisar ya ce sakamakon matsalar lalacewar, gaba ɗaya yankin arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas na ƙasar sun kasance cikin duhu, da uwa uba ƙarin tsanani na tsadar rayuwa.
Ya ƙara da cewa abin takaici ne yadda matsalar ke faruwa a daidai lokacin da ministan wutar lantarkin ke ba wa 'yan Najeriya tabbacin ingancin samar da wutar, abin da ya sa har gwamnati ta ce ya sa dole ta ƙara kuɗin wutar ga masu amfani da ita na rukunin farko ko babban layi (Band A ).
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa ma'aikatu da wasu hukumomin gwamnatin Najeriya garambawul, inda aka haɗe wasu aka kuma ƙirƙiru wasu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ya fitar ta ce Tinubu ya ba da umarnin rusa hukumar bunƙasa yankin Neja-Delta da kuma ma'aikatar wasanni.
Bayo Onanuga ya ce a madadin haka, yanzu za a ƙirƙiri ma'aikatar bunƙasa yankuna da za ta kula da hukumomin yankunan da ake da su.
Sai kuma hukumar kula da wasanni ta ƙasa da za ta maye gurbin ma'aikatar wasanni.
Haka nan, majalisar zartarwa ta amince da haɗe ma'aikatar al'adu da ma'aikatar yawon buɗe ido wuri guda.
Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Najeriya ta saki babban jami'in kamfanin kuɗin kirifton nan na Binace, wanda ta gurfanar gaban shari'a bisa zargin laifin halatta kuɗin haram, domin ya je a duba lafiyarsa a waje.
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar zagon-ƙasa, EFCC, ce ta sanar da sakin Mista Tigran Gambaryan, wanda ke tsare tun watan Afirilu, saboda tsananin rashin lafiya da yake fama da shi a cewarta.
Lauyar hukumar ta EFCC, R. U. Adagba ce ta sanar da kotun tarayyar da ke shari'ar, dakatar da tuhumar, a lokacin zaman kotun, yau Laraba a Abuja, saboda rashin lafiyar jami'in.
Sai dai kuma lauyar ta shaida wa kotun cewa, hukumar ta EFCC, za ta ci gaba da tuhumar da take yi wa kamfanin na Binance Holdings Limited.
Abin da ba a sani ba shi ne yadda za a ci gaba da shari'ar ba tare da mutumin da ke wakiltar kamfanin ba.
Can a baya alƙalin kotun, Justice Emeka Nwite, a karo biyu ya ƙi amsa buƙatar lauyoyin jami'in kamfanin ta bayar da belinsa, bisa dalilan yuwuwar cewa zai iya guduwa daga Najeriya, to amma lauyoyin suka kafe cewa lafiyar Mista Gambaryan ta taɓarɓare a lokacin da yake tsare.
A watan Fabarairu ne hukumomin Najeriya suka kama Mista Gambaryan, wanda ɗan ƙasar Amurka ne tare da shugaban kamfanin a Afirka, Nadeem Anjarwalla, yayin ziyara a Najeriyar kan wasu batutuwa na dokokin aiki da suka shafi kamfanin na Binance.
Sai dai Anjarwalla, ya tsere daga hannun 'yansanda, ya bar ƙasar, bayan da aka kai shi masallaci ya yi sallah.
Ana tuhumar Gambaryan ne da laifin halarta kuɗaɗen haram da kuma gudanar da kamfanin hada-hadar kuɗaɗe wanda ba shi da lasisi a ƙasar, zargin da ya musanta.
Asalin hoton, STATE HOUSE
Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya ya ce yawan mutanen da suka rasu sakamakon hatsarin tankar mai sun ƙaru zuwa 181.
Mallam Umar Namadi ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a ranar Talata, yana mai cewa mutum 80 ne ke asibiti a yanzu.
Sai dai ya ce adadin zai iya ci gaba da ƙaruwa saboda yanayin jinya.
"Dalilin da ya sa adadin ke sauyawa shi ne har yanzu akwai waɗanda suka ji raunin amma kuma suna gida ba su je asibiti ba," a cewarsa bayan ganawa da Tinubu.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta kafa kwamatin bincike, sannan shugaban ƙasa ma ya bayar da umarnin yin binciken "domin ganin hakan ba ta sake faruwa ba".
A makon da ya gabata ne tankar man ta faɗi a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura, inda mutane suka taru domin kwasar fetur ɗin da take ɗauke da shi kafin wuta tashi kuma ta kashe kusan mutum 100 a lokacin.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 23/10/2024 – BBC
