Aƙalla mutum 30 ne suka rasu sakamakon ƙwacewar da wata babbar mota mai ɗauke da kayan siminti ta Ɗangote mai amfani da iskar gas ta yi ta kuma shiga cikin dandazon motoci a Karu da ke kan titin Abuja zuwa Keffi da yammacin ranar Laraba.
Shehu Ɗalhatu wanda shi ne mai kula da yankin Kubo a hukumar kula da ingancin ababan hawa ta Abuja, VIO ya ce "kawo yanzu mutum 30 ne suka rasu sakamakon hatsarin inda wasu kuma ke asibiti suke samun kulawa."
Waɗanda suka shaida faruwar al'amarin sun shaida wa BBC cewa hatsarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Laraba, sun ce wata babbar mota ce ɗauke da kayan siminti da kuma ke gudu na wuce ƙima ta shiga cikin motoci.
Shaidun sun ce al'amarin ya shafi motoci kusan 20, inda mutanen da ke motocin wasu suka tsira da ƙunar wuta amma wasu kuma ba su kai labari ba.
"Motar ta zo a guje saboda an nemi a tsayar da ita saboda lokacin shigowar manyan motoci bai yi ba kuma hakan ne ya sa ta shiga cikin motoci inda ta rinƙa bangazar motoci kawai sai ta kama da wuta saboda tana amfani da iskar gas." Mathew Ɗanjuma Yare wanda shi ne kansila na Nyanya.
Shaidar ya ƙara da cewa "mutane dai da mu kwashe a nan mutum takwas sun mutu a take sannan an kwashe mutum huɗu da suka ƙone da ba za a gane su ba. Haka kuma an kwashe mutanen da dama zuwa asibiti to ba mu sani ba ko sun mutu a asibitin." In ji kansila Ɗanjuma.
Bisa doka dai bai kamata manyan motoci su shiga birnin Abuja ba har sai bayan ƙarfe 10 na dare.
Rundunar ƴansanda babban birnin Najeriya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida da ƙonewar motoci 14 sakamakon hatsarin a yankin Karu.
Kakakin rundunar ƴansandan SP Josephine Adeh wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ibtila'in ya faru ne a jiya laraba da ƙarfe 6:58 na yamma bayan wata babbar mota da ke maƙare da siminti ta ƙwace ta faɗa kan motocin da ke maƙale cikin cunkoso ababen hawa kusa da gadar Nyanya.
Ta ce ma'aikatan ceto sun yi gaggawar isa wurin da ke cike da baƙin hayaƙi da tsananin zafi domin ceto waɗanda suka maƙale inda ta ce an samu nasarar zaƙulo mutane shida, sai dai bayan kai su asibiti likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
Kakakin rundunar ta kuma ce tare da haɗin gwiwar ƴansanda da ma'aikatan kashe gobara da ma wasu jam'ian tsaro an samu nasarar kashe gobarar.
Rundunar ƴansandan Abuja ta kuma miƙa ta'aziyyarta ga iyalan waɗanda iftila'in ya shafa tare da tabbatarwa da alumma cewa za a gudanar da cikakken bincike kan sanadin iftila'in da kuma yadda za a kare sake afkuwar irinsa.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Yadda motar Ɗangote ta afka kan motoci ta kashe mutum 30 a Abuja – BBC
