An ɗage taron mahaddata Al-Kur’ani da aka shirya yi a Abuja – BBC

Asalin hoton, Getty Images
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III ya ce yawan masu son halartar taron mahaddata al-Qur'ani fiye da yadda aka tsara shi ne dalilin dage taron.
A wata sanarwa da aka aike wa manema labarai, Sarkin Musulmin wanda shi ne jagoran taron ya ce da farko dai an tsara cewa za a gayyaci mutum dubu 60 ne domin halartar taron amma kuma mutane fiye da dubu 509,000 suka yi rijista.
“An tsara gayyatar mutum dubu 60 da suka hada da dubu 30 mahaddata da kuma sauran mahalarta su ma dubu 30.
To amma yanzu mutum 500,000 suka yi rijista kuma dandalin taron yana daukar mutum dubu 60. Hakan ne ya sa muka dage taron zuwa wani lokaci a gaba.” In ji samaras..
Kafin dagewar an dai saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 da ranar da za a yi taron da ake sa ran zai samu mahalarta waɗanda mahaddata Qur'ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Najeriya.
Daga karshe sanarwar ta ce dagewar za ta bai wa masu tsaron damar sake shiri domin karbar baki daga gida da waj.
Asalin hoton, Getty Images
Taron dai wanda tuni allunan tallansa suka cika manyan titunan birnin Abuja ya kankane kafafen watsa labarai da na zumunta, inda wasu ke yabo wasu kuma ke kushe shi.
Da ma tun kafin yanzu batun taron na mahaddatan ya janyo muhawara, inda wasu ke sukar kalmar da aka yi amfani da ita ta "festival" da ke nufin da "biki", sannan wasu ke dangantaka al'amarin da siyasa, wasu kuma suke kallonsa a matsayin wani abu baƙo a addinin Musulunci.
Manufar taron dai kamar yadda shafin tsara taron ya ce shi ne fito da irin jajircewar da mahaddata al-qur'ani suka yi shekara aru-aru.
"Al'ummar Najeriya daga sassa da ƙabila daban-daban na ƙasar sun sadaukar da rayuwarsu wajen haddace Qur'ani a ɗaruruwan shekaru" In ji shafin da ke tsara taron.
Saboda haka wannan taron zai zama wani dandamali na karrama makaranta da marubuta al-qur'ani mai girma. Sannan wata mahaɗa ce da ke nuna yadda al'adu da ƙabilun Najeriya daban-daban ke karanta da mu'amala da Qur'ani da irin karin harshensu sannan bisa al'adunsu." In ji shafin.
Shafin ya kuma lissafa ƙarin wasu muhimman abubuwan da za a yi a lokacin taron kamar haka:
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds