Asalin hoton, Other
Fadar shugaban Najeriya ta yi gargadi game da shirin kai hare-haren ta'addanci a Abuja babban birnin Tarayyar kasar a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
A sakamakon haka kuma hukumar lura da shige da fice ta kasar ta ce ta girke jami'anta a kan iyakokin kasar da kuma a fadin kasar a wani mataki na shirin ko-ta-kwana.
Hukumar shige da ficen ta ambato wata sanarwa daga fadar shugaban kasar tana cewa ta samu bayanan sirri da ke nuna wasu 'yan ta'adda daga kasar Mali na shirin shiga kasar ta kan iyakar Najeriya da Nijar domin su kaddamar da hare-hare a babban birnin kasar.
A wata wasika da hukumar shige da fice ta rubuta ranar 23 ga watan Disambar shekarar 2021 mai taken "Hare-haren ta'addaci a Abuja" dauke da sa hannun Kwamanda mai lura sintirin kan iyakokin kasar, Mista Edirin Okoto, zuwa ga duka Kwamandojin yankunan da sauran jami'an da ke kan iyakokin kasar da filayen saukar jiragen saman kasar, ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar kai munanan hare-hare a Abuja tsakanin 17 zuwa 31 ga watan Disambar 2021.
Wasikar, wadda aka rubuta a madadin shugaban hukumar shige da ficen Malam Idris Jere, ta kuma bayyana cewa wani Drahmhane Ould Ali, da aka fi sani da Mohammed Ould Sidat, dan kasar Algeria da ke samun goyon bayan wani dan Najeriya Zahid Aminon ne ke jagorantar shirin kai hare-haren.
Kuma bayanan sirrin sun yi nuni da cewa mutanen biyu na kan hanyarsu ta shiga Najeriya daga kasar Mali ta cikin Jamhuriyar Nijar a cikin wata farar a-kori-kura kirar Toyota Hilux mail lamba AG157EKY
Wasu jaridun Najeriya sun rawaito cewa rundunar sojin kasar da sauran hukumomin tsaro da suka hada da hukumar shige da ficen sun tsaurara matakan tsaro a fadin birnin na Abuja sakamakon wannan gargadi daga fadar shugaban kasa.
Birnin na Abuja ya shafe watanni biyu cikin shirin ko-ta-kwana tun bayan samun wasu bayanan sirri na yiwuwar kwararar 'yan ta'adda cikin birnin, a cewar rahotanni.
A baya bayan nan ma sai da gwamnan jihar Naija a arewacin kasar Abubakar Sani Bello ya yi zargi tare da gargadin cewa 'yan ta'adda sun mamaye wasu sassan jihar inda suke cin karen su babu babbaka, kuma ba da dadewa ba za su iya shiga cikin birnin na Abuja mai nisan kilomita 120 daga jihar.
A shekarar 2011 wani harin bam da aka kai a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 21 da jikkatar mutum 60.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
'Yan ta'addan Algeria da Mali na shirin kai hare-hare a Abuja – BBC
