Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ci gaba da kawo muku jerin rahotanni kan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, yau Laraba mun dubi batun tsadar haya da kuma gidaje ne a birnin.
Kasancewar Abuja fadar gwamnati ce, masu haya na biyan makudan kudade domin zama a sassa daban-daban na birnin.
A manyan unguwanni kamarsu Maitama da Asokoro, dillalan gidaje na cewa ana biyan kudin haya kamar Naira milyan takwas zuwa tara kan ko wane gida mai daki uku a ko wace shekara.
Wani dillalin gidaje Aliyu Abubakar yace "a unguwanni irinsu Jabi kuwa ana biyan kudin haya Naira Miliyan biyar ko kuma miliyan hudu da dubu dari biyar kan gida mai daki uku a ko wace shekara".
A unguwanni da ke wajen Abuja kuwa kamar su Mararraba da Nya-nya, ana samun gidajen hayar da dan sauki kamar daga Naira dubu 500 zuwa sama kan ko wani gida mai daki biyu da falo duk shekara.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Abin da ba ku sani ba kan tsadar haya da gidaje a Abuja – BBC
