Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 24/01/25
Usman Minjibir, Annur Muhammad da Isiyaku Muhammed
Masu bin wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Asalin hoton, Reuters
Rahotonni sun ce Ukraine ta kai hare-haren jirage marasa matuka 121 kan matatar man Rasha, a daya daga cikin hare-hare mafiya girma da ta kai tun bayan fara yakin.
Bidiyon harin da aka yada – wanda BBC ta tantance sahihancinsa – ya nuna yadda hayaki na turnuke saman matatar a gundumar Ryazan da ke kudu maso gabashin birnin Moscow, wanda Ukraine ta ce ta kai wa harin.
Rasha ta ce ta kakkabo jirage marasa matuka 121 a gundumominta 13, ciki har da Ryazan da Moscow, amma ba ta bayar da rahoton kowace irin barna ba.
Haka ma can a Ukraine, hukumomin kasar sun ce an kashe mutum uku tare da raunata guda a lokacin da jirgin Rasha maras matuki ya kai hari kan wani gida a gundumar Kyiv.
Asalin hoton, Zamfara State Gov.
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bai wa ɗaliban jihar su 16 da suka karanci aikin jinya, a jami'ar Sudan aiki.
A ranar Alhamis ne gwamnan ya gabatar wa ɗaliban takardunsu na shaidar kammala karatu da jami'ar ta aiko musu a fadarsa gwamnati da ke birnin Gusau.
Cikin wata sanarwar da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ya ce a 2023 ne gwamnatin jihar ta kwaso ɗaliban Zamfara 66 da ta tura Sudan domin karatu bayan ɓarkewar rikicin ƙasar.
''16 daga cikin ɗaliban masu karantar aikin jinya ne da ke shekarar ƙarshe a karatunsu, waɗanda jarrabawar ƙarshe ce kawai ta rage su kammala karatun, inda gwamnatin jihar ta ɗauki matakin taimaka wa ɗaliban'', in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta haɗa kai da hukumar gudunarwar jami'ar, domin bai wa ɗaliban 16 damar rubuta jarrabawar tasu ta ƙarshe, wadda aka yi a Najeriya.
Daga nan kuma jami'ar ta aika wa ɗaliban takardun shaidar kammala karatun nasu, wadda kuma gwamnan ya gabatar musu a lokacin da ya yi musu albishirn ba su aikin a gwamnatin jihar.
Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta tabbatar da mutuwar gwamnan lardin Arewacin Kivu a gabashin ƙasar, sakamakon yaƙi da 'yantawayen M23.
Kakakin sojojin ƙasar, Janar Sylvain Ekenge, ya ce gwamnan sojin, Manjo Janar Peter Cirimwami Nkuba ya mutu ne sakamakon harbin bindiga a fagen daga a ranar Alhamis.
Gwamnan ya ziyarci sojojin da ke fagen daga a garin Kasengezi da ke kusa da Goma, babban birnin Arewacin Kivu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 200,000 da gidajensu, sakamakon ƙazancewar rikici a gabashin Kongo, kuma alkaluman sun ruɓanya adadin da aka fitar a makon daya gabata.
Faɗan da ake tafkawa a garin Sake da kudancin Kivi sun tilasta wa dubban mutane gudun hijira da neman mafaka a Goma.’
'Yantawayen M23 na ta fafatawa da sojojin Kongo da ƙoƙarin mamaya a Goma da arewacin Kivu.
Asalin hoton, Getty Images
Wata mata a Faransa wadda ta daina amincewa da mijinta ta samu nasara a wata shari'a da aka tafka a kotun kare hakkin bil'adama ta nahiyar Turai.
Matar, wadda aka kira ta da suna H.W, wadda ke zama a wani gari da ke kusa da birnin Paris na ƙasar Faransa, ta auri mijinta mai suna JC ne a shekarar 1984.
Sun haifi ƴaƴa huɗu, ciki har da wata yarinya mai lalurar da ke neman kulawa a koda yaushe.
Auren nasu ya fara samun matsala ne a shekara ta 1992 lokacin da matar ta fara samun lalura.
Bayan shekara biyu, H.W ta daina kwanciyar aure da mijin nata, sannan a shekarar 2012 ta shigar da buƙatar neman raba auren, bayan mijin ya fara tsangwama da 'cin zarafinta'.
A ranar Alhamis, kotun da ta yanke hukunci ta goyi bayan H.W, inda ta kafa hujja da cewa bai kamata a zargi matar da aikata wani laifi ba saboda kawai ta ƙi amincewa da mijin nata.
Shari'ar ta haifar da zazzafar muhawara kan ƴancin mata a cikin gidajen aure a Faransa.
Asalin hoton, PA Media
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce kungiyar na neman dan wasan gaba ''ido rufe'' a wannan lokaci na musayar 'yan kwallo a watan Janairun da muke ciki, idan har tana son kai bententa.
Kungiyar na fama da karancin 'yan wasan gaba bayan da Bukayo Saka ke doguwar jinya sannan a baya-bayan nan shi ma Gabriel Jesus ya fara jinya.
Kaka uku kenan a jere Arsenal na kokawar lashe kofin Premier, amma sai raunukan manyan 'yan wasanta ya shafi yunkurin nata.
A yanzu haka kungiyar na matsayi na biyu da tazarar maki shida tsakaninta da Liverpool ta daya a kan teburi.
A yanzu dai an yi waje da kungiyar a gasar FA, sannan Newcastle ta doke ta da ci 2-0 a wasan farko na matakin dab da karshe a gasar Carabao.
Asalin hoton, @BUHARISALLAU
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya koma kasar bayan gurfana a gaban wata kotu a birnin Paris na kasar Faransa.
Cikin wani bidiyo da tsohon mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna lokacin da tsohon shugaban kasar ke sauka daga jirgi a jihar Katsina.
A farkon makon nan ne tsoffin shugabannin Najeriya biyu, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari suka bayyana a gaban wata kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Paris na a ƙasar Faransa domin ba da bahasi dangane da kwangilar aikin gina cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambilla da ke jihar Taraba.
Wani kamfani mai suna Sunrise Power ne dai ya kai gwamnatin Najeriya ƙara kan saɓa ƙa'idojin kwangilar, inda yake neman gwamnatin ta biya shi dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 300 a matsayin diyya na asarar da aka janyo masa.
Tsoffin shugabannin biyu, sun bayar da shaida kan abin da suka sani dangane da kwangila da aka bayar da ita a 2003, lokacin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.
Asalin hoton, Getty Images
Wani binciken BBC ya gano sama da mutum 60 da aka kashe a hare-haren Isra’ila a kudancin Lebanon a watan Satumban bara fararan-hula ne – ciki har da kananan yara 23.
Harin, wanda a ka kai ta sama kan wani rukunni gidajen bene a kauyen Ain El Delb ya yi ajalin mutum 73 a jimillance.
Wannan hari shi ne mafi muni da aka kai a lokaci guda lokacin yakin Isra’ila da Hezbollah.
Rundunar Sojoji Isra’ila ta ce ta kai harin ne kan Kwamandojin Hezbollah kuma galibi mayakansu ta kashe, ciki harda wani babban kwamanda.
Sai dai binciken BBC ya tabbatar da cewa cikin mutum 60 da aka kashe, shida kadai ke da alaka da Hezbollah.
Asalin hoton, AFP
Shugaban sojin Isra'ila ya yi murabus daga mukaminsa, saboda abin da ya kira gazawarsa a harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai cikin kasar, wanda kuma shi ne sanadiyyar yakin Gaza.
Cikin wata wasika da ya aike wa ministan tsaron kasar, Laftnar Janar Herzi Halevi ya amince cewa rundunar sojin Isra'ila, IDF, ta ''Gaza aiwatar da hakkin da ya rataya a kanta na kare 'yan Isra'ila''
"Gazawata da ta janyo wannan mummunan abu a kullum yana ta bibiyata, kuma zan ci gaba da nadama har karshen rayuwata,'' in ji shi.
Jim kadan bayan aika wasikar tasa, sai shugaban rundunar IDF mai kula da yankin kudancin kasar, Manjo Janar Yaron Finkelman, shi ma ya ayyana sauka daga mukaminsa, yana mai cewa shi ma ya gaza a hakkin da ya rataya a kansa na kare yammacin Negev da al'ummar yankin.
Saukar jagororin IDF din na zuwa ne kwana uku bayan fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da fara sakin Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su a lokacin harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana buƙatar dala miliyan 910 domin shawo kan matsalar jin ƙai a arewa maso gabashin Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan rahoton haɗin guiwa da gwamnatin tarayya da majalisar dinkin duniya suka fitar a watan Nuwanba na 2024 wanda ya nuna cewa ƙasar na fuskantar matsalar yunwa, inda mutane sama da miliyan 30 aka yi hasashen cewa za su fuskanci ƙarancin abinci a 2025.
A wajen taron ƙaddamar da kundun tsare-tsaren ayyukan jin ƙai na arewa maso gabas da ya gudana a jiya Alhamis a Abuja, MDD ta jaddada cewa "Mutane kusan miliyan takwas na buƙatar agaji a jihohin, Borno da Adamawa da Yobe, inda ke akwai mutane miliyan 2.3 da suka rasa muhallansu.
MDD ta ce rikicin da ake fuskanta a ƙasashen Ukraine da Gaza da Sudan ne suka dauke hankalin duniya daga na arewa maso gabashin Najeriya.
A cewar takardun Majalisar Dinkin Duniya, bukatar kudi da ake da ita a yanzu ya sanya matsalar jin ƙai a arewa maso gabas ta zama mafi tsada a yammaci da tsakiyar Afirka; kuma mai yiwuwa ya zarce na Chadi, Mali, Burkina Faso, da Nijar.
Jakadan Japan a China ya ce an yanke hukuncin kisa kan wani dan China da aka samu da laifin kashe wani yaro dan makaranta a Japan a watan Satumban bara.
Ya kashe yaron dan shekara 10 ne ta hanyar daba masa wuka a hanyarsa ta zuwa makaranta a birnin Shenzhen.
Wannan hukunci na zuwa ne kwana guda bayan yankewa wani dan China makamancin wannan hukunci kan kai harin wuka a wata motar makaranta a birnin Suzhou.
A lokacin harin wata mata ‘yar China ta rasa ranta a kokarin kare Fasinjoji ‘yan Japan da aka yi kokarin kashewa.
Dukkanin laifuka biyu sun girgiza ‘yan Japan mazauna China.
Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta Taliban a Afghanistan sun yi alla-wadai da bukatar sammacin kama shugabanninta, da aka gabatar a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, wanda suke cewa siyasa ce kawai.
Ma’aikatar ketaren Taliban ta ce wannan wani shiri ne mara alkibila da adalci a cikinsa.
A jiya Alhamis, babban mai gabatar da kara a Kotun ICC, Karim Khan ya nemi kotu ta bada sammacin kama jagoran Taliban, Haibatullah Akhundzada da babban mai shari’a Abdulkarim Haqqani kan cin zarafi mata, manya da kanana.
Asalin hoton, DAUDA LAWAL DARE/FACEBOOK
Hukumomi a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun mayar da martani game da bayanin da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi cewa akwai yara dubu 250 da ke fama da matsananciyar yunwa daga cikin yara miliyan daya da dubu dari biyu da aka yi nazari a kansu a jihar.
Gwamnatin jihar ta ce lokacin da ta karbi mulkin jihar ta tarar da harkokin kula da lafiya ba kamar yadda ta yi tsammani ba, amma a cewar kwamishinan yada labaran jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa sun dauki matakai dai-dai gwargwado.
"Yanzu haka gwamnati na gyara asibitocin matakin farko da suke a karkara guda 62 wadanda yawancinsu angama gyaransu kuma yanzu haka ana raba maganin tamowa a asibitin."
Gwamnatin ta kuma yi kira ga iyayen yara da su riƙa zuwa wadannan asibitoci domin karɓar maganin tamowar kyauta.
Asalin hoton, DR
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugaban jam'iyar APC, Abdullahi Umar Ganuje a matsayin shugaban kwamitin gudanarwar hukumar kula da filayen sama, FAAN.
Tinubu ya kuma naɗa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, kuma ɗan takarar gwamnan Kano a zaɓen 2023, Nasiru Gawuna a matsayin shugaban hukumar bankin bayar da rancen sayen gida, wato Morgage bank.
Haka kuma shugaban ya naɗa sakataren jam'iyar APC na ƙasa, Sanata Bashiru Ajibola a matsayin shugaban hukumar gudanarwar NSDC.
Mai magana ba shugaban ƙsar shawara kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ne ya sanar da naɗe-naɗen a cikin wata sanarwar da ya fitar a yau Juma'a.
"Shugaban Tinubu ya naɗa shugabannin hukumar gudanarwa 42 na ma'aikatun gwamnatin tarayya da sakataren hukumar gudanarwa na gidajen yari da hukumar shigi da fici da kuma ta hukumar tsaro da kai dauki ta Civil Defence," Cewar sanarwar.
Sannan shugaban ya naɗa kanen ministan ayyuka, Augustine Chukwu Umahi, a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
Wani alkali a Kenya ya yi gargadin zai garkame wani babban jami’in ‘Yansanda a gidan kaso, idan ya ki bayyana gaban kotu a ranar Litinin, domin jin bahasi kan zargin su da hannu sace-sacen mutane da ake fama da su a dan tsakanin nan, sai dai ‘yansandan sun musanta hannu a lamarin.
Batan dabon da gwamman matasan da ke adawa da gwamnati suka a lokacin zanga-zangar shekarar da ta gabata ta janyo sukar gwamnati ta kowanne bangare.
Asalin hoton, Getty Images
Ma’aikatar noma ta Najeriya ta ce za ta gina ɗakunan gwaje-gwajen nau’o’in ƙasa a ƙananan hukumomin jihar Kano 44.
Ma’aikatar ta ce ɗakunan binciken za su taimaka wa manoma wajen tantance irin shukar da ta dace da ƙasar gonakinsu ta yadda za a samu yabanya.
Ƙarƙashin shirin an zaɓi jihohin Kano da Oyo don yin gwaji, inda ake fatan samar da na’urorin zamani da ƙwararrun ma’aikata.
Alhaji Isa Isayaku Hotoro babban jami’i a ma’aikatar harkokin noma da bunƙasa samar da abinci ta tarayya da ke jihar Kano shi ne ya wakilci ministan ma’aikatar a wajen wani taron tattaunawa game da yadda za a samar da ɗakunan a Kano.
Asalin hoton, Reuters
A gobe Asabar ne Hamas za ta fitar da sunayen mutum huɗu da za ta saka cikin mutanen ta yi garkuwa da su a Isra'ila, a wani mataki na cika sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakaninta da Isra'ila.
Za a yi musayar su ne da Falasɗinawa 180 da suke fursuna a Isra'ila, kamar yadda aka yi musayar Isra'ilawa uku da Falasɗinawa 90 a zagayen farko na musayar.
An shiga yarjejeniyar ne domin kawo ƙarshen yaƙin da aka fara a ranar 7 ga Oktoban 2023 lokacin da Hamas ta kai hari a Isra'ila, inda ta kashe kusan mutum 1,200, sannan ta yi garkuwa da mutum 251.
A mayar da martani da Isra'ila ta yi, ta kashe sama da mutum 47,000, mafi yawanci fararen hula, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta fitar.
Yanzu ana jiran Hamas ta bayyana sunayen sauran fursunonin yaƙin da za su saka nan da mako biyar da za a yi ana ɗabbaƙa yarjejeniyar.
Daga cikin waɗanda ke hannun Hamas har da iyalan Bibas – mahaifi da mahaifiya da yara biyu, ciki har da Kfir mai wata goma da haihuwa lokacin da aka yi garkuwa da su.
Asalin hoton, EPA
Wani ɗanmajalisar Amurka ya kawo ƙudurin da zai ba Shugaban Ƙasa Donald Trump damar zarcewa wa'adin mulki na uku a matsayin shugaban ƙasa.
Andy Ogles, ɗanmajalisa mai wakiltar Tennessee ne ya gabatar da ƙudurin domin gyara ga sashe na 22 da aka taɓa gyara a baya domin hana shugabancin ƙasar sama da wa'adi biyu.
Sabon ƙudurin zai ba shugaban ƙasa damar yin wa'adi uku, matuƙar guda biyu ne ya yi a jere da duka ukun ba, wanda daga gani an san domin Trump ya tsara.
"Wannan gyarar za ta ba Shugaban Ƙasa Trump damar yin wa'adi na uku a mulki, domin cigaba da mulkin ba gani ba sao, wanda shi ƙasarmu ke buƙata a yanzu," in ji shi.
Sai dai gyara kundin tsarin mulkin Amurka na da wahala, inda ake buƙatar biyu bisa ukun ƴan majalisa da majalisar dattawa su amince. Hakan ke nufin ko da ya samu goyon bayan dukkan ƴan majalisar jam'iyyar Republican – wanda zai yi wahala – ba za su cika abin da ake buƙata ba.
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Sahel (AES), ta samar da sabon fasfo da zai maye gurbin wanda ƙasashen uku cewa da Nijar, Mali da kuma Burkina Faso ke amfani da shi mai tambarin Ecowas.
Sun ɗauki wannan matakin ne a ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da ficewarsu daga ƙungiyar ta yammacin Afirka.
Sai dai domin kawo sauƙi ga ƴan ƙasashen na mallaka fasfon, masu riƙe da fasfo mai tambarin ECOWAS za su cigaba da amfani da shi har zuwa ƙarshen wa’adinsa inda ƙungiyar ta ce ta ɗauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da ƴanci da walwalar al’ummomin yankin na ƙasashen na AES.
Asalin hoton, Reuters
Jagorar ƴan adawar Belarus da ke gudun hijira ta yi kira ga ƙasashen yammacin duniya da su yi watsi da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ƙarshen mako.
Svetlana Tikhanovskaya ta shaida wa BBC cewa shugaba Alexander Lukashenko yana da haɗari kamar na shugaban Rasha Vladimir Putin, inda ta kira shi ɓurɓushin ƴan mulkin danniya, da maƙure jama’a.
Mista Lukashenko ya shafe fiye da shekara 30 a karagar mulki kuma bayan zaɓen da ya gabata a shekarar 2020 ana zargin ya murƙushe zanga-zangar kan tituna ta masu zargin an yi maguɗin zaɓe.
Tikhanovskaya ta ce yanzu abu ne mai matuƙar haɗari ga jama’a su iya yin zanga-zanga a ƙasar Belarus.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.