Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/12/2024
Abdullahi Bello Diginza
Firaministan Albania ya ce gwamnati za ta toshe kafar sada zumunta ta TikTok a kasar na tsawon aƙalla shekara ɗaya daga watan Janairu.
Tun lokacin da wani bidiyo ya bayyana a watan da ya gabata na kisan wani yaro ɗan shekara 14 da wani dalibi ya yi ta hanyar yi masa yankan rago ne gwamnatin kasar ta fara nazarin toshe kafar.
Karo na hudu kenan da irin wannan kisan ke faruwa a wannan shekarar, lamarin da ya haifar zazzafar muhawara.
Kamfanin TikTok ya ce zai nemi ƙarin bayani kan yunƙurin matakin daga gwamnatin Albania
An yi bikin ƙarin girma ga shugaban Chadi Mahamar Idriss Deby daga Janar zuwa mukamin Mashal – wanda shi ne ƙololuwar mukamin a tsarin aikin soji.
Tuni majalisar dokokin kasar ta Chadi ta amince da dokar yin ƙarin girma ga shugaban. Kuma a ranar aka yi bikin ƙarin girman a fadarsa.
A 2020 aka ayyana mahaifinsa marigayi Idriss Deby a matsayin muƙamin Mashal lokacin da yana shugaban ƙasa kafin mutuwarsa.
Mahamar Deby ya kwashe mulki ne tare da taimakon wasu manyan sojojin Chadi, kuma aka tabbatar da shi a matsayin shugaban da aka zaɓa a watan Mayun 2024, wanda ƙasashen duniya da dama ke ganin an murkushe ƴan'adawa.
Asalin hoton, Twitter
Rahotanni daga tsakiyar Mali sun ce masu iƙirarin jihadi sun kai hari a wasu ƙauyuka, inda suka kashe mutane 20.
Mali ta shafe shekaru tana ƙoƙarin kawar da ayyukan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.
Gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta koma neman tallafin Rasha wajen yaƙi da mayaƙan, kuma ta tilastawa dakarun Faransa barin ƙasar.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron yana wata ziyara a Habasha, inda zai gana da firaiministan ƙasar, Abiy Ahmed.
Gwamnatin Najeriya ta yi martani ga zargin da maƙwabciyarta Nijar ta yi cewa tana neman tarwatsa ƙasar ta hanyar taimakawa ƴanbindiga.
Ma'aikatar harakokin wajen Najeriya ta bayyana abin da ta kira "babbar damuwa ga zargin cewa dakarun Faransa a arewacin ƙasar da ke shirin hargitsa gwamnatin Nijar."
"Wadannan zarge-zargen ba su da tushe kuma ya kamata a yi watsi da su gaba daya." kamar yadda ma'aikatar harakokin wajen Najeriya ta bayyana a wata sanarwa a ranar Asabar, kwanaki uku bayan Nijar ta kira babban jami'in diflomasiyyar Najeriya domin nuna fushinta.
A ranar Alhamis gwamnatin Nijar ta yi zargin cewa wasu dakaru a Najeriya sun taimaka wa mayakan Lakurawa wajen kai wa bututun man kasar da Benin hari.
A cikin sanarwar da Najeriya ta fitar ta musanta zargin, tana mai cewa, "babu wani taimako da maharan suka samu daga hukumomin Najeriya ko kuma nuna goyon bayansu.
Asalin hoton, @officialABAT
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya soke ayyukan da ya tafi yi a jiharsa ta Legas domin karrama wadanda suka mutu sakamakon turmutsutsin da ya janyo hasarar rayuka a Abuja da jihar Anambra.
Aƙalla mutum 10 sun mutu, ciki har da ƙananan yara, yayin da da dama suka samu raunuku sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a cocin Catholic da ke unguwar Maitama a Abuja.
Cikin wata sanarwa da rundunar 'yansandan birnin Abuja ta fitar, ta ce cikin waɗanda suka mutu har da ƙananan yara huɗu, yayin da mutum takwas suka samu munanan raunuka, kuma suke karɓar magani a asibiti.
Can ma a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin ƙasar rahotonni na cewa wasu mutane sun mutu bayan wani turmutsutsu da aka samu a wajen rabon tallafi a jihar a ranar ta Asabar.
Sanarwar da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta ce shugaban ya soke kallon wasan kwale-kwale da aka tsara zai yi a Ikoyi. Sannan ya yi wa mamatan addu'a tare da fatan murmurewa ga waɗanda suka jikkata.
Yan Najeriya na fama da matsin rayuwa sakamakon matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka kan tattalin arziki waɗanda suka kai ga janye tallafin man fetur wanda kuma ya haddasa tsadar kayan abinci da sufuri.
Jami'an hukumar kashe gobara a Brazil sun ce aƙalla mutum 22 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙasar.
Lamarin ya faru ne cikin dare a jihar Minas Gerais da ke kudu maso gabashin ƙasar, lokacin da tayar wata motar bas ta fashe a lokacin da take tsaka da tafiya.
Shaidu sun ce motar ta tsallaka zuwa ɗaya gefen inda ta yi karo da tirela ɗauke da dutwasu, sanna ta kama da wuta.
Mayaƙan IS sun kashe sojojin Pakistan 16 a wani hari da suka kai wani ƙaramin sansanin soji da ke kan iyaka a arewa maso yammacin ƙasar.
Haka kuma wasu ƙarin sojojin biyar sun jikkata a harin – wanda ya kasance ɗaya daga cikin munanan hare-hare cikin watannin baya-bayan nan.
Ƙungiyar Taliban ta Pakistan ta ce ta kai samame cikin dare a kudancin Waziristan – kusan kilomita 40 daga kan iyakar Afghanistan.
Rahotonni sun ce kusan mahara 30 ne suka kai wa sansanin hari.
A baya-bayan nan an samu ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi a kan iyakokin ƙasashe masu maƙwabtaka da Afghanistan tun bayan da Taliban ta karɓe koma iko da ƙasar.
Asalin hoton, Magnum Photos
Amurka ta amince da sayar wa Masar kayan aikin soji da ya kai fiye da dala biliyan biyar
Masar ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke samun tallafin soji daga Amurka tun bayan sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila a 1979.
Matakin na zuwa ne duk kuwa da zarge-zargen take haƙƙin bil-adama da aka yi wa Masar a ƙarƙashin mulkin shugaba Abdel Fattah al-Sisi.
Ƙungiyar Amnesty International ta yi ƙiyasin cewa akwai fursunonin siyasa fiye da 6,000 da ke tsare a gidajen yarin Masar.
Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta yi watsi da kalaman da wani babban jami'in tsaron Amurka ya yi na cewa shirin makamanta masu linzami ka iya zama barazana ga Amurka.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce tana gudanar da shirin nata ne domin kare kanta daga barazanar ƙasashe maƙwabta.
A baya-bayan nan ne dai mataimakin mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro, Jon finer ya yi iƙirarin cewa ƙera makaman linzami masu cin dogon zango da Pakistan ke yi, waɗanda ka iya kai wa ga wajen nahiyar Asiya da kuma mallakar makamin nukiliya ka iya zama barazana ga Amurka.
A ranar Laraba ne Amurka ta bayyana ƙaƙaba wa wasu kamfanonin Pakistan huɗu da wasu ƙungiyoyi da ke taimaka wa shirin ƙasar na samar da makamai masu linzami.
Asalin hoton, FCT Police Command
Aƙalla mutum 10 sun mutu, ciki har da ƙananan yara, yayin da da dama suka samu raunuku sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a cocin Catholic da ke unguwar Maitama a Abuja.
Lamarin ya faru ne ya faru ne ranar Asabar da safe lokacin da mutane suka yi dafifi a harabar cocin domin karɓar kayan tallafi da ta alƙawarta raba wa marasa ƙarfi da tsofaffi.
Cikin wata sanarwa da rundunar 'yansandan birnin Abuja ta fitar, ta ce cikin waɗanda suka mutu har da ƙananan yara huɗu, yayin da mutum takwas suka samu munanan raunuka, kuma suke karɓar magani a asibiti.
'Yansandan sun ce jami'an tsaro sun samu nasarar korar duka mutanen da suka taru a cocin waɗanda ta ce sun kai fiye da mutum 1,000.
Firimiyan jihar Saxony-Anhalt da ke Jamus, Reiner Haseloff, ya ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da aka kai kasuwar Kirsimeta ta Magdeburg ya kai mutum biyar.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan ya halarci kasuwar, Mista Haseloff ya ce waɗanda suka jikkata kuwa sun kai 200.
41 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, yayin da 90 suka samu munanan raunuka, sai kuma 80 da suka samu ƙananan raunuka, kamar yadda kafar yaɗa labarai da ARD ta ruwaito.
A ranar Juma'a da daddare ne dai wani wani mutum ya tuƙo motar tare da kutsawa cikin kasuwar mai cike da cunkoson jama'a.
Asalin hoton, Defence HQ/X
Rundunonin sojin Najeriya sun yi wa ɗaruruwan manyan hafoshin ƙarin girma a wani mataki na inganta ƙwazon aiki.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta ƙasar ta fitar ta a shafinta na X, ce ta yi wa manyan hafsoshi 35 masu muƙamin Birgediya Janar ƙarin girma zuwa matsayin Manjo Janar, sannan ta yi wa masu muƙamin Kanal 73 ƙarin girma zuwa matsayin Birgideiya Janar.
A nata ɓangare ita ma rundunar sojin sama ta ƙasar ta sanar da yi wa manyan hafsoshi 19 zuwa matsayin Air Vice Marshals, sannan ta yi hafsoshi 33 ƙarin girma zuwa Air Commodores.
Sai kuma rundunar sojin ruwa da ta yi wa manyan hafsoshinta 146 ƙarin girma.
Rundunar sojin ruwan ta ce ta ƙara wa hafsoshi 24 girma zuwa 'Rear Admiral', sai 26 zuwa matsayin Commodore, da kuma 96 da aka ƙara wa girma zuwa matsayin 'Captain'
Asalin hoton, Yahaya Bello/Facebook
Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta saki tsohon gwamnan jihar Kogi, Yayaya Bello daga gidan yarin Kuje da ke Abuja, bayan cika sharuɗan beli da babbar kotun Abuja ta gindaya masa a makon da ya gabata.
Sanarwar sakin tsohon gwamnan na ƙunshe cikin wata sanarwar da kakakin hukumar kula da gidajen yarin ƙasar reshen Abuja, Adamu Duzu ya fitar ranar Juma'a, kamar yadda jaridun ƙasar suka ambato.
“An saki Yahaya Bello, bayan cika sharudan beli, kuma babban koturolan gidajen yari mai lura da Abuja, Ajibogun Olatubosun, ya je gidan yarin domin tabbatar an bi duka sharudan da suka dace wajen sakin tsohon gwamnan,'' in ji sanarwar.
A makon da ya gabata ne mai shari'a MaryAnne Anenih ta babbar kotun Abuja ta bayar da belin Yahaya Bello kan kuɗi naira miliyan 500.
Sannan cikin sharuɗan har da gabatar da mutum uku da za su tsaya masa, waɗanda suka mallaki kadarori a manyan unguwann masu daraja a Abuja, kamar Maitama ko Asokoro da Guzape.
Haka kuma kotun ta buƙa tsohon gwamnan ya miƙa mata takardun tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen waje.
Hukumar EFCC mai yaƙin da cin hanci da rashawa ce dai ta gurfanar da Yahaya Bello tare da wasu mutum biyu, kan kan laifuka 16 ciki har da zargin karkatar da kuɗi naira biliyan 110 daga asusun gwamnatin jihar Kogi in da yake gwamnan jihar.
To sai dai tsohon gwamnan ya musanta duka zarge-zargen da EFCCn ke yi masa a gaban kotun.
Kalli hotunan yadda kasuwar Kirsimeti ta Magdeburg a Jamus ta wayi gari, bayan harin motar da aka kai mata ranar Juma'a da daddare.
Kasuwar – mai cike da cunkoson jama'a – a yanzu ta zama tamkar kufai, yayin da 'yansanda suka zagayeta.
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Hotuna a kafafen sada zumunta sun nuna yadda motar ta shige rumfunan kasuwar a guje.
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Ya zuwa yanzu, mutum biyu sun mutu sannan da dama sun jikkata.
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
'Yan sandan ƙasar sun ce sun kama mutum guda da suke zargi da hannu a harin
Asalin hoton, EPA
Tuni dai 'yansanda suka yi wa kasuwar ƙawanya
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Dauda Lawal/Facebook
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya ce har yanzu yana kan matsayarsa, cewa ba zai yi sulhu da ƴan fashin daji ba.
Yayin zantawarsa da BBC gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne ganin cewa a bayan an sha yin sulhu da 'yan bindigar, amma ba sa mutunta alƙawurran da aka yi da su a baya.
''An yi sulhun nan a baya ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma an kasa cimma ake abin da ake so'', in ji gwamnan.
''Saboda haka ina nan a kan bakata, maganar sulhu da 'yanbindiga babu ita'', kamar yadda ya bayyana
Ya ce duk da haka, ƙofa a buɗe take ga ƴan fashin da ke neman hanyar da za su dawo su rungumi zaman lafiya, ta hanyar miƙa wuya kuma su kawo makamansu ga hukuma.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da 'yanbindiga ke yawaita kai hare-hare tare da yin garkuwa da mutane.
Hukumomi a ƙasar Guatemala sun ce sun kuɓutar da yara 160 daga gonar wata ƙungiyar Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi da ake zargi da lalata da kananan yara.
Ministan harkokin cikin gida (Francisco Jimenez) ya ce 'yan sanda sun kai samame gonar da ke garin Oratorio a yankin kudu maso gabashin birnin Guatemala.
Kungiyar ta zargi mahukuntan ƙasar da cin zarafi mai alaƙa da addini.
Membobin ƙungiyar sun koma Guatemala ne shekara 10 da suka gabata daga Canada, inda a can ma suke fuskantar bincike kan zargin cin zarafi ta hanyar lalata da kananan yara.
Asalin hoton, Reuters
'Yan sanda a kasar Jamus sun kama wani ɗan ƙasar Saudiyya bayan da wata mota ta afka cikin masu sayayya a wata kasuwar Kirsimeti mai cike da cunkoson jama'a a gabashin birnin Magdeburg.
Hotuna a kafafen sada zumunta sun nuna yadda motar ta shige rumfunan kasuwar a guje.
Shugaban, Rainer Haseloff ya ce wannan bala'i ne da ya faɗa wa birnin Magdeburg da ma ƙasar Jamus baki ɗaya.
Ya zuwa yanzu, mutum biyu sun mutu sannan da dama sun jikkata.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake kai hare-hare da mota tare da kashe mutane a kasuwar ta Kirsimeti a Jamus
Ko a shekarar 2016, wani mutum mai alaƙa da ƙungiyar IS ya kutsa da mota cikin wata kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin tare da kashe mutum 12.
Masu bin shafin BBc Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan lokaci.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku domin kawo muku labaran halin da duniya ke ciki.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.