Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 18 ga watan Janairun 2025.
Haruna Kakangi, Muhammad Annur
Asalin hoton, UNI ABUJA
Jami'ar Abuja za ta bude cibiayr koyar da harshen China (Mandarin) da kuma al'adun kasar ta Sin.
Shugabar jami'ar Farfesa Aisha Maikudi ce ta bayyana haka lokacin da ta karbi bakuncin tawagar wasu dalibai na sashen koyon aikin jarida da sadarwa na jami'ar Tsinghua ta China, a jiya Juma'a.
Farfesa Aisha ta ce nan ba da dadewa ba jami'ar ta Abuja wadda ta ce tana da alaka da China bisa dadaddiyar alaka tsakanin Najeriya da China za ta bude wannan cibiya.
Ta kara da cewa tuni daman wasu daliban jami'ar ta Abuja ke yin wasu kwasa-kwasai na harshen na Sinanci – Mandarin.
Asalin hoton, FRSC
Ana fargabar mutane da yawa sun rasu wasu kuma sun ji rauni yayin da suke kokarin dibar man fetur daga wata tankar mai da ta fadi a kwanar Dikko da ke, babban titin Abuja zuwa Kaduna, a jihar Naija.
Rahotanni na cewa lamarin wanda ya faru yau Asabar, ya kasance ne lokacin da tankar da ke gudu ta fadi man ya zube, mutane suka je suna kwasar man sai motar ta yi bindiga wuta ta tashi.
Wutar ta kone mutane da dama da ke kwasar man yayin da wadanda suke nesa da ita kuwa suka ji rauni.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Bologi Ibrahim, wanda shi ne kakakin gwamnan jihar ta Naija, Mohammed Bago, wanda ke cikin tawagar gwamnan da ke kan hanyarta ta zuwa Suleja da Tafa domin duba ayyuka, ya tabbatar mata da aukuwar lamarin.
Kakakin ya ce gwamnan ya nuna alhininsa a kan hadarin sannan ya bayar da umarni ga jami'an tsaro su tabbatar da tsaro a wajen sannan dukkanin hukumomin gwamnatin jihar su yi abin da ya wajaba a kai.
Ko a watan Oktoba na shekarar da ta wuce an samu makamancin wannan hadarin a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa inda sama da mutum 170 suka mutu, wasu wajen 50 suka ji rauni, a fashewar tankar, lokacin da wasunsu ke kwasar mai.
Asalin hoton, Getty Images
Kafar yada labarai ta gwamnatin Iran ta ce wani danbindiga ya harbe wasu manyan alkalai biyu a cikin kotun kolin kasar da ke Tehran, babban birninta.
Kafar ta ce maharin ya kuma jikkata wani alkalin da wani dogari.
Maharin wanda ba a kai ga gane shi ba zuwa yanzu, ya kuma hallaka kanshi bayan harbin.
Ba a dai san dalilin kai harin ba, to amma dukkanin alkalan biyu da aka kashe sun yi kaurin suna wajen gallazawa da kisan masu hamayya da gwamnatin kasar ta Iran a shekarun 1980 da 1990.
Daya daga cikin alkalan ma ya taba tsira daga wani yunkuri na kashe shi, shekara talatin da ta gabata.
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a India ta samu wani matashi da laifi a shari'ar da aka tuhume shi da yi wa wata likita mai neman sanin makamar aiki fyade da kuma kisanta a wani asibiti da ke Kolkata a watan Agusta da ya wuce.
Kisan ya zanyo zanga-zanga a fadin kasar wadda ta dade likitoci na ta yi, inda suke bukatar lalle sai an yi wa abokiyar aikin nasu adalci, tare kuma da bada karin kariya ga masu aikin lafiya.
Kwana daya da faruwar lamarin an kama matashin da aka samu da laifin wanda mai aikin sakai ne a asibitin, inda kuma aka tsare shi a ofishin 'yansanda na Kolkata.
Ɗaya daga cikin fitattun mawaƙa mata da suka yi fice cikin shekarun baya a arewacin Najeriya, Salmai Albasu ta ce tana alfahari da irin gudunmawar da ta bayar wajen wayar da kai don bunƙasa ilmi da yaƙi da fyaɗe.
Zabiyar ta yi fice tun daga shekarun 1970 wajen wayar da kai don jama'a su rungumi ilmi, su tura ƴaƴansu makaranta.
Asalin hoton, X/EFCC
Hukumar yaƙi da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ce ta kama mutum 25 waɗanda take zargin masu damfara ne ta intanet a wani wuri da ake kyautata zaton wurin horas da damfara ne, a birnin Benin na jihar Edo.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, EFCC ta ce ta samu nasarar yin hakan ne a ranar Alhamis ta hanyar amfani da jami'anta na shiyyar Benin.
Bayanin ya ƙara da cewa "kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri ne da ta tattara, waɗanda ke nuna cewa ana amfani da wani gini a matsayin wurin koyar da damfarar yahoo ko kuma horas da masu son ƙwarewa a sauran hanyoyin damfara ta intanet.
Hukumar ta ce ta kuma gano wasu kaya a lokacin samamen nata, waɗanda suka haɗa da dalla-dallan motoci guda shida, da kwamfutoci da kuma wayoyi.
Najeriya dai ta yi ƙaurin suna a harkar damfara ta intanet a duniya.
Asalin hoton, Getty Images
TikTok ya bayyana cewa zai 'daina aiki' a Amurka daga ranar Lahadi, matuƙar dai gwamnatin shugaba Joe Biden ba ta ɗauki matakin hana dakatar da shi ba.
Hakan na zuwa ne bayan Kotun ƙolin ƙasar, a ranar Juma'a ta amince da matakin Majalisar dokokin Amurka na haramta ayyukan manhajar, har sai idan kamfanin da ya mallaki manhajar – wanda ke da alaƙa da China – ya amince zai sayar da ita ga wani kamfanin Amurka, bisa dalilai na tsaro.
Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce ba za ta bayar da umarnin amfani da dokar ba, to amma TikTok ya ce idan har da gaske ne to ya kamata gwamnati ta fitar da sanarwa domin tabbatar wa kamfanonin Apple da Google matsayar tata.
Donald Trump, wanda za a rantsar a matsayin shugaban Amurka a ranar Litinin – ya nuna aniyar ganin ba a tabbatar da haramcin amfani da mahajar ba.
Majalisar Dokokin Amurka ce ta yanke shawarar haramta TikTok a ƙasar ne bisa dalilai na tsaro, inda ta ce akwai yiwuwar gwamnatin China na amfani da mahajar wajen tattara bayanan mutanen Amurka, wanda take amfani da shi wajen yaɗa manufa.
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar rarraba lantarki ta Najeriya (TCN) ta sanar da cewa wasu mutane sun ɓarnata tare da sace kayan wuta da ke samar da lantarki ga wasu sassa na Abuja, babban birnin ƙasar.
Sanarwar da hukumar ta fitar a jiya Juma'a ta ce "an lalata layin wutar lantarkinta na 132kV da wayoyin ƙarƙashin ƙasa waɗanda ke kai lantarki zuwa cikin ƙwaryar Abuja da unguwannin da ke kewaye, lamarin da ya kawo katsewar lantarki".
Lamarin dai ya jefa unguwannin Abuja da dama cikin duhu, tare da haifar da wahalahalu ga al'umma.
Sanarwar, wadda ta samu sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Ndidi Mbah, ta ce wayoyin su ne ke kai lantarki ga cibiyoyin rarraba lantarki na kamfanin AEDC domin samar da lantarki ga al'umma.
"Lamarin wanda ya faru a kusa da Millenium Park da ke Abuja, ya shafi fiye da kashi 60 cikin ɗari na lantarkin da ake samar wa birnin," in ji sanarwar.
Bayanin ya tabbatar da cewa maɓarnatan sun sace wayoyin lantarki da sauran kayan wuta da dama.
Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da Maitama, da Wuse, da Jabi, da Life Camp, da Asokoro, da Utako da kuma Mabushi.
Hukumar ta TCN ta ce ta tura jami'anta domin yin gyara a inda aka sace kayan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Babu karin bayanai
Asalin hoton, X/BRICS News
Gwamnatin Brazil ta sanar da cewa Najeriya ta amince ta shiga cikin ƙungiyar ƙasashen duniya da ake yi wa laƙabi da BRICS.
Brazil, wadda ita ce ke shugabantar ƙungiyar a 2025, a cikin wata sanarwa, ta bayyana cewa Najeriya "ta ƙasance ƙasa da ke ƙara ƙarfafa hulɗar dangantaka tsakanin ƙasashen ɓarin kudancin duniya da kuma sauya salon shugabanci", wanda abu ne da Brazil ke bai wa muhimmanci.
"A matsayinta ta ƙasa ta shida mafi yawan al'umma a duniya, kuma mafi yawan al'umma a Afirka, kuma ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka, Najeriya na da kamanceceniyar manufofi da ƙasashen ƙungiyar," kamar yadda sanarwar ta ma'aikatar harkokin waje ta Brazil ta sanar.
BRICS, ƙungiya ce ta ƙasashen da suka haɗa ba Brazil, Rasha, Indiya, China, Afirka ta kudu, Masar, Habasha, Indonesia, Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Ana wa ƙungiyar kallon kini ta ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi ta duniya, wato G7.
Asalin hoton, Reuters
Hukumomi a Kyiv, babban birnin ƙasar Ukraine sun ce wani hari da Rasha ta kai kan birnin a cikin dare ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu.
Makamin ya faɗa kan birnin ne, kafin hukumomi suka kaɗa ƙaraurawar gargaɗi, daga nan ne kuma aka ci gaba da jin saukar makamai a birnin.
Mahukunta sun ce an kai harin ne da miyagun makamai, kuma sun buƙaci al'ummar birnin su nemi mafaka a wuraren ɓoyo na ƙarƙashin ƙasa.
Magajin garin birnin Kyiv, Vitaly Klitschiko ya ce lamarin ya tilasta rufe ɗaya daga cikin tashoshin jiragen ƙasa na birnin.
Bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna wata mota na ci da wuta, yayin da ruwa ke malala a kan wani titi.
Wannan ne hari na biyu mafi muni da aka kai kan birnin na Kyiv a cikin wannan wata na Janairu.
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar ministocin Isra'ila ta kammala amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wadda ta ƙunshi musayar waɗanda Hamas ke garkuwa da su da kuma sakin fursunoni Falasɗinawa da ake riƙe da su a Isra'ila.
Matakin na zuwa ne bayan shafe sa'o'i ana tattaunawa har zuwa cikin tsakiyar dare.
Ɗaya daga cikin ministoci masu tsattsauran ra'ayi ya ce zai ajiye muƙaminsa domin nuna adawa da batun, yayin da ɗaya kuma ya ce shi ma zai fice daga gwamnatin idan ba a ci gaba da yaƙin ba bayan ƙarewar matakin farko na yarjejeniyar, wanda zai ƙare cikin mako shida.
Yarjejeniyar za ta fara aiki ne a gobe Lahadai.
Da farko za a saki mutum uku da Hamas ke garkuwa da su yayin da ita kuma Isra'ila za ta saki Falasɗinawa fursunoni da take tsare da su.
Haka nan Isra'ila za ta fara janye dakarunta daga Gaza.
Muna yi muku maraba da zuwa shafin BBC Hausa da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Yau Asabar, 18 ga watan Janairu, 2025.
Za ku iya bayyana ra'ayinku kan labaran da muke kawo muku a shafukanmu na sada zumunta: facebook, X, Instagram da YouTube.
Haka nan za ku iya shiga tasharmu ta WhatsApp.
Da fatan za ku kasance tare da mu daga farko har ƙarshe.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya – BBC
