Asalin hoton, NDHQ
Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta shaida wa BBC Hausa cewa ta karbi kashin farko na sojoji mata 100 daga cikin 300 da aka aika hanyar Kaduna zuwa Abuja domin wanzar da tsaro.
A ranar Laraba ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da aike sojoji mata 300 zuwa hanyar domin shawo kan matsalar masu garkuwa da mutane a kan hanyar.
An kwaso sojoji matan ne daga runduna ta daya ta sojin kasar da ke jihar Kaduna, kuma kuma an hada su da rundunar sojojin kasar ta mata domin yin aiki tare.
Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya karbi tawagar matan, wadda ita ce rukunin farko da za su zauna a masaukinsu da ke Kakau a kan hanyar ta Abuja.
El-Rufa'i ya ce matsalar tsaro da ta addabi hanyar za ta zama tarihi a nan ba da jimawa ba domin kuwa matan za su yi kokari wajen kawar da ita.
Asalin hoton, NDHQ
Ya kuma tabbatar musu da samun cikakken goyon baya daga gwamnatin jihar Kaduna yayin gudanar da ayyukansu.
A wata tattaunawa da ya yi da Hausa, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya ce matan duka gwaraza ne da suka yi gwaninta a kan ayyukansu a wasu fannonin daban-daban.
"Rundunar sojin Najeriya za ta turo jami'an tsaro har 300 a nan gaba, amma a ranar Laraba mun karbi kashin farko na sojoji 100, nan da 'yan kwanaki sauran za su iso jihar Kaduna," in ji Aruwan.
Ya kara da cewa: "Soja kuda soja ne za su kara karfi ne da kuma taimako ga wadanda suke ayyuka ta sama da ta kasa."
Asalin hoton, NDHQ
Da aka tambaye shi game da ikirarinsu na cewa hanyar ta yi lafiya, ya ce "Babu wanda ya ce kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba ne, maganar Hausawa ce ta idan kana da kyau ka kara da wanka, kuma ana hakan ne domin nasarar da ake samu ta dore."
Mr Samuel Aruwan ya ce akwai bayanai da yawa da ba za a iya bayani ba a kafafen yada labarai, amma babu shakka wadannan sojoji mata za su kara taimakawa a yakin da ake yi da masu garkuwa da mutane a kan wannan hanya.
Wasu yankuna da dama na jihar Kaduna sun daɗe da yin bankwana da zaman lafiya saboda hare-haren ƴan fashi, sannan ita ma babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama tarkon mutuwa ga matafiya.
Masu garkuwa da mutane sun sace matafiya da dama a kan hanyar yayin da suka kashe da yawa daga cikinsu.
'Yan Najeriya da dama da ke bin hanyar sun ƙaurace mata inda suka gwammace su bi jirgin ƙasa su kuwa masu hali suna hawa jiragen sama domin gudun masu garkuwa da mutane.
Bin hanyar na nufin ko dai a isa inda za a je lafiya ko kuma tsautsayi ya sa a ci karo da ƴan bindiga da ke shiga da mutane cikin daji suna neman kuɗin fansa.
Jami'an tsaro da gwamnatoci sun sha cewa suna bakin ƙoƙarinsu domin wanzar da zaman lafiya a kan hanyar, sai dai hakan bai hana ci gaba da satar mutane ba.
Sai dai masana harkokin tsaro na ganin wannan mataki ka iya rage ko kuma kawar da matsalar da ke faruwa a kan hanyar idan aka bai wa sojojin mata 300 isassun kayan aiki da hakkokinsu a kan lokaci.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Abuja-Kaduna: Abin da ya kamata ku sani kan sojoji mata 300 da aka aika hanyar don wanzar da tsaro – BBC
