An rufe kasuwannin Abuja uku bayan kashe mutum biyar a rikicin Dei-Dei – BBC

Ministan Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Mohammed Bello, ya tabbatar da cewa an kashe mutum biyar a wani rikici da ya ɓarke a Kasuwar Dei-Dei a ranar Laraba.
Kazalika Minista Bello ya shaida cewa an rufe kasuwa uku da suke unguwar har sai baba ta gani.
A ranar Laraba, 18 ga watan Mayun 2022 ne wata tarzoma da ta barke a kasuwar kayan gini da ke unguwar ta Dei-Dei, inda mutane da dama suka jikkata.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa tarzomar ta samo asali ne bayan wata babbar mota ta take wata mata da ke kan acaɓa, lamarin da ya sa aka ƙone babur din, wanda kuma ya fusata ƴan acaba suka shiga ƙone shaguna da farfasa ababen hawa.
Ministan Abuja ya bayar da umarnin rufe kasuwar ne bayan da ya ziyarci wajen da abin ya faru, ƙarƙashin rakiyar kwamishinan ƴan sanda na Abujar Sunday Babaji, da shugaban hukumar DSS na biirnin da kuma wasu manyan jami'an hukumar birnin tarayyar.
A yayin ziyarar ministan ya ce: "A yau na ɗauki lokaci kusan awa biyu ni da jami'an tsaro na Abuja muka tafi Dei-Dei, inda muke da manyan kasuwanni kamar uku, don ganin ɓarnar da ɓata-gari suka yi.
"Kuma na zo ne sakamakon samun rahoton da na samu na rikicin, da kuma yadda mutane suka dinga yada hotuna da labari na ƙarya a kan batun cewa ƙabilu da 'ƴan Arewa suna ƙone-ƙone," in ji shi.
Asalin hoton, @OfficialFCTA
Minista Bello ya bayyana yadda abin ya faru inda ya ce wata mata ce ta hau acaɓa, sai babur ɗin da take kai ya yi karo da wani babur ɗin daban sai matar ta faɗi ƙasa, a bisa tsautsayi sai wata mota ta taho ta take kanta, nan take ta mutu.
Sanadin mutuwar tata sai jama'a suka razana, aka so a afka wa mai babur. Shi kuma sai ƴan uwansa masu acaɓa suka kai masa ɗauki.
Kafin a ankara ɓata-gari suka fito suka fara ƙona motocin mutane tare da shiga kasuwar sayar da katakwaye, "kuma galibi masu sayar da katako ƴan shiyyar kudu maso gabashin Najeriya ne kamar yadda aka sani," a cewar ministan.
"Hakan ne ya sa aka ɗauka cewa faɗa ne tsakanin ƴan arewa da ƴan kudu, kuma sanadiyyar haka aka yi ɓarna da yawa.
"Da na je na samu shugabannin al'ummun, kamar yadda aka sani Abuja ta haɗa ƙabilu da dama da suka zo neman na kai. Shi ya sa na tafi da wuri don tabbatar da halin da ake ciki.
"Abin takaicin dai ɓata-gari, ƴan ƙwaya su ne suka ta'azzara abin."
Ministan ya ce ya tattauna da shugabannin al'ummun, waɗanda suka tabbatar masa cewa sun daɗe suna zama lafiya da juna kuma sun ce min su ya su za su tabbatar sun gano wadanda suka tayar da hargitisn.
Sun kuma fada wa ministan za su dage don ganin ɓata-gari ba su lalata musu zamantakewa ba da kare faruwar irin hakan a gaba.
Bello ya ce za a ƙara kai jami'an tsaro da dama wurin don a dawo da doka da oda.
Kazalika ya ce ya bayar da umarnin gyara tsarin unguwar da hanyoyin shiga kasuwannin kansu.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds