Asalin hoton, FB/Aminu Dahiru
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da salon jagorancin shugabanta, Abdullahi Umar Ganduje.
Wannan dai shi ne karon farko da APC ta gudanar da taron ƙolin, tun bayan rantsar da gwamnatin shugaba Tinubu a watan Mayun 2023.
Hakan na nufin cewa tsohon gwamnan na jihar Kano zai ci gaba da jagorancin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a yi babban taronta na ƙasa, inda za a zaɓi cikakken shugaba.
A watan Agustan 2023 ne kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya tabbatar da Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na riƙo na ƙasa, bayan ajiye aikin shugaban jam'iyyar da ya gabace shi, Sanata Abdullahi Adamu.
Babban taron ƙoli na jam'iyyar APCn na ƙasa ya mayar da hankali ne kan nazari a game da abubuwan da suka shafi jam'iyyar, da nasarorin da ta samu da kuma ɓangarorin da take buƙatar gyara.
Haka nan kuma mahalarta taron sun kaɗa ƙuri'ar yabawa da shugabancin shugaban ƙasar, Bola Tinubu.
Asalin hoton, Getty Images
Sai dai kuma wani abu da ya ja hankali shi ne yayin da shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa da ke zauren taron, akwai wasu ƙusoshin jam'iyyar da ba a gan su a wurin taron.
Tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi na daga cikin waɗanda suka ƙaurace wa taron.
Dangane da rashin halartar taron da tsohon shugaban na Najeriya Muhamamdu Buhari ya yi, BBC ta tuntuɓi Malam Garba Shehu, tsohon mai taimaka masa a harkokin ƴanjarida.
"Shugaba Buhari ba mamba ba ne na majalisar ƙolin jam'iyyar APC ba. Taron masu ruwa da tsaki wanda aka yi ranar Talata ya kamata a ya halarta. Kuma abin da ya sa bai samu halartar taron na ranar Talata ba shi ne ranar Litinin ne aka aike masa da gayyatar taron amma wasiƙar ba ta tarar da shi ba sai ranar Talata da rana. Ka ga ai ba zai iya barin Daura har ya je Abuja ya halarci taron ba ko da kuwa yana da jirgin kansa." In ji Malam Garba Shehu.
Sai dai kuma Malam Garba ya ce duk da Buhari bai samu halartar taron ba amma zuciyarsa na tare da taron jam'iyyar.
"Shugaba Buhari da shi aka kafa jam'iyyar APC. Sannan jam'iyyar ta ba shi damar shugabancin Najeriya har karo biyu saboda haka lallai har yanzu shugaba Buhari ɗan jam'iyyar APC ne cikakke ko da kuwa bai halarci babban taronta na ƙasa ba." In ji Garba Shehu.
Gwamnonin da suka halarci taron kawo yanzu dai sun haɗa da gwamnonin jihohin Edo, Benue, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Niger, Lagos, Kogi, Ogun, Imo, da kuma mataimakin gwamnan jihar Ebonyi da kuma tsaffin gwamnonin jihohin Kogi, Kebbi, Neja, Zamfara da Filato.
Babu dai wani dalili da ya fito filin na rashin halartar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i taron na APC.
Sai dai kuma a baya-bayan nan Nasir El-Rufa'i ya ja zare da jam'iyyar tasa bisa abin da ya kira sauka daga kan aƙidar da aka kafa ta da kuma gazawar jagorancin jam'iyyar wajen kiran taron masu ruwa da tsakin.
To amma El-Rufa'i ya nanata cewa yana cikin jam'iyyar ta APC daram babu inda za shi tun da yana ɗaya daga cikin mutanen da suka rattaba hannu aka kafa ta.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon ministan sufuri na Najerita, Rotimi Amaechi babu cikakken bayani na dalilin rashin halartar taron.
A baya-bayan nan dai ba a cika jin amon Amaechi ba, inda a wata tattaunawa da ya yi da BBC a kwanakin baya inda ya ce "idan akwai abu guda ɗaya da na koya daga wurin shugaba Buhari, shi ne rage yawan surutu domin ya taɓa faɗa min cewa 'Amaechi ba don abinci kawai aka yi ciki ba',"
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
APC ta amince Ganduje ya ci gaba da jagorancinta – BBC
