Yayin da babbar sallah ke ƙaratowa kuma al'ummar Musulmi ke ƙara ƙaimi wajen sayen dabbobi domin yin layyar, farashin dabbobin na ci gaba da hauhawa sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita musamman a Najeriya.
Wakilan BBC na wasu biranen Najeriya da suka zagaya wasu kasuwannin sayar da dabbobi sun ce sun ga dabbobi masu yawa a ɗaure amma babu masu saya sosai saɓanin a shekarar da ta gabata.
"Bana al'amarin ba a cewa komai. Ga dabbobi lafiyayyu amma kuma jama'a ba a saya sakamakon rashin kuɗi saboda dabbobin sun yi tsadar da ba a taɓa ganin irinta ba a ƴan shekarun nan." In ji Alhaji Ɗantsoho Goron Dutse, mai sayar da dabbobi a kasuwar Goron Dutse da ke birnin Kano.
BBC ta samo farashin dabbobin daga kasuwar Goron Dutse da kuma Ƙofar Ruwa kamar haka:
Farashin Raguna: Ragon da a bara aka sayar da shi naira dubu 50 yanzu ya koma naira dubu 100 zuwa dubu 150. "Farashin raguna ya fara daga naira 75,000 zuwa naira 700,000."
Farashin Shanu: Ana sayar da sa ko saniya mafi ƙanƙanta a kan naira dubu 350,000 inda ma fi girma kan kama kan naira miliyan 2.5.
Farashin Raƙumi: Ana sayar da raƙumi mafi ƙanƙanta naira 300,000 inda ake sayar da manya a kan naira miliyan 1.7.
A birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ma haka al'amarin yake.
Kuma wakilinmu na Legas ya leƙa mana kasuwar Iponri daura da unguwar Surulere a cikin birnin Legas wasu daga cikin kasuwannin dabbobin da ke birnin da kuma ke samun dabbobin daga arewacin Najeriya.
"Farashi na bana ya sha bamban saɓanin yadda aka saba saye a baya. Yanzu ragon da ka saba saye a baya naira 100,000 yanzu ya ninka sau uku sai dai ka ji ana cewa naira 300,000". In ji wani mai sayar da raguna.
"Rago dai ga shi nan. Farashinsa ya kama daga naira 100,000 ne zuwa naira 300,000 inda ma fi girman ragon ke kai wa naira 700,000". Kamar yadda wani mai sayen ragunan ya shaida wa BBC.
"Akwai kuma na talakawa daidai kuɗinsu wanda ya kama daga naira 125,000 zuwa 200,000".
A Abuja, babban birnin Najeriya ma farashin bai bambanta da na sauran biranen ba, inda ake sayar da ragunan daga naira 80,000 zuwa naira 1,000,000 a waɗansu daga cikin kasuwannin birnin kamar Deidei da Apo da Anagada.
"Kun san ƴan Abuja ba sa sayen tumaki ko awaki. Daga raguna sai shanu. Kuma farashin raguna na farawa ne daga naira 80,000 zuwa naira 1,000,000. Amma fa za a iya samun fiye ko ƙasa da haka tunda dai kasuwa ce." In ji wani mai sayar da dabbobi a kasuwar Anagada.
Bayanai sun nuna cewa farashin shanu a kasuwannin na Abuja ya fara ne daga naira 500,000 zuwa naira miliyan 3.5.
Ƴan Najeriya da dama dai na ta dasa ayoyin tambaya dangane da dalilan da suka sa al'amura suka tsefe musamman a wannan shekara, wadda ba ma dabbobi ba hatta sauran kayayyaki na neman gagarar al'ummar ƙasar musamman marasa da masu matsakaicin ƙarfi.
BBC ta tambayi Alhaji Ɗantsoho Goron Dutse dangane da dalilan da suka haifar da tsadar dabbobi a bana.
"Gaskiya mu ma ba mu taɓa ganin shekarar da dabbobi suka yi kuɗi kamar bana ba kuma ni dai a fahimtata dalilai biyu ne suka haifar da wannan yanayi. Dalilan kuwa su ne: tsadar sufuri da tsadar abincin dabbobi."
Tsadar sufuri:
Alhaji Ɗantsoho ya ce "tun bayan cire tallafin man fetur kuɗin sufuri ya yi tashin gwauron zabbi. Ka ga kenan idan muka je muka sayi dabbobin nan a kasuwannin ƙauyuka, dole ne mu yi amfani da mota wajen fito da su zuwa kasuwannin birni.
To kuma saboda sayen mai masu motar sun ƙara kuɗin mota. Saboda haka dole ne kuɗin da aka kashe a sufuri ya fita a jikin dabbobin."
Tsadar abinci:
Alhaji Ɗantsoho Goron Dutse ya ce "yanzu abincin dabbobi ya fi na mutane tsada, wataƙila saboda daga jikin na mutanen ake samun na dabbobin. Misali, yanzu buhun dussa ya tashi daga naira 3,000 zuwa naira zuwa naira 20,000. Shi kuma buhun ƙaiƙayi wanda ake sayar da shi a bara naira 8000 ya koma naira 15,000."
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Babbar Sallah: Yadda tsadar raguna ke tsorata masu son layya a Najeriya – BBC
