Boko Haram: Shin Abuja na fuskantar barazanar 'yan ƙungiyar? – BBC

Asalin hoton, Getty Images
Masana harkar tsaro a Najeriya sun bukaci mahukunta da su gudanar da bincike a kan wata wasikar gargadi da aka ce ta fito daga hannun hukumar kwastam ta kasar, wadda ke ankarar da jami`anta da ke Abuja da wasu jihohi makwabta a kan barazanar hari daga kungiyar Boko Haram.
Masanan sun bayyana cewa abin mamaki ne yadda irin wannan wasikar gargadi ta fito daga hukumar kwastam, sabanin wasu hukumomi da aka sani, wadanda aikinsu ne bincike a kan harkar tsaro, irin hukumar tsaron farin kaya ta DSS da bangarorin binciken sirri na sojoji da `yan sanda.
Sun kara da cewa ko da maganar barazanar ta kasance gaskiya, to kamata ya yi a ce hukumar kwastam ta danka wa hukumomin asiri bayanin.
Dr Kabiru Adamu na kamfanin da ke nazari a kan harkokin tsaro a Najeriya da yankin Sahel, ya shaida wa BBC cewa bai kamata mahukunta su yi wasa da barazanar da ke kunshe cikin wasikar ba, ganin cewar mayakan Boko Haram na shirin kaddamar da hari a kan Abuja da jihohin Nasarawa da Kogi.
"Da bukatar hukumomi wadanda ke da hakki su bincika su gani ya aka yi irin wannan wasika da bayanai masu muhimmanci har ya fito haka. Idan muka duba abin da wasikar ke tattare da shi, ba za mu ce ya ba mu mamaki ba don muna sane cewa 'yan bindiga da barayi suna amfani da irin wadannan dazuzzuka a matsayin sansani," a cewar Dr Kabiru.
Masanin tsaron ya kara da cewa: "Abu na biyu cewa da aka yi suna shirin kawowa Birnin Tarayya hari, lallai wannan abu ne mai tayar da hankali don a baya sun kawo irin wadannan hare-hare kuma mun ga aibun da suka yi."
Ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakin kwantarwa da mazauna Abuja hankali da kuma ba su kariya.
Sai dai yana wannan kira ne bayan da rundunar sojin kasar ta ce jami`anta suna cikin shirin ko-ta-kwana don dakile duk wata barazana da ka iya tasowa a birnin na Abuja.
A cewarta, ta ga wasikar kuma har ta hada kai da wasu hukumomi domin daukar matakin da ya dace.
Kwamanda Abdussalam Sani, kakakin cibiyar da ke samar da bayanai a kan arangamar da sojojin Najeriya ke yi a sassan kasar, ya shaida wa BBC cewa "wannan sabon abu da ya fito ya kara mana kwarin gwiwa da kuma kara sa kaimi a duk inda ya kamata musamman a garin Abuja da kewaye."
Dangane da zargin cewa ko masu barazanar kai harin suna da alaka da `yan kungiyar Darus Salam, wadanda sojojin Najeriyar suka suka ce sun tarwatsa kwanan nan a karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa kuwa, Kakakin sojin cewa ya yi ba za su iya musantawa ko karyatawa ba, amma suna kan bincikawa.
Tun fitar wasikar gargadin, hukumar kwastam ta yi gum da bakinta, lamarin da ya bude kafar yada baza ji-ta-ji-ta game da sahihancin wasikar.
Hatta BBC ta yi kokarin tuntubar kakain hukumar Joseph Attah, amma shiru kake ji.
Kodayake, daga bisani wasu kafofin yada labarai sun ambato shi yana cewa sam, da shi da hukumar kwastam duka babu abin da suka sani game da wasikar gargadin.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds