Coronavirus: Buhari ya kara mako daya kan dokar kulle a Abuja da Legas da Ogun – BBC

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaba Muhammadu Buhari ya kara mako daya kan dokar kullen da aka saka a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja.
Sai dai daga karfe 9:00 na safiyar Litinin 4 ga watan Mayu, za a sassauta dokar, inda mazauna jihohin za su fara fita daga karfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na yamma.
Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya a daren Litinin.
Buhari ya ce: "Dokar kulle da ake kai a yanzu za ta ci gaba da aiki a Abuja da Legas da Ogun har sai wadannan sabbin matakan sun fara aiki ranar 2 ga watan Mayun 2020 da karfe 9 na safe."
"Duba da wannan da kuma shawarwarin kwamitin fadar shugaban kasa na musamman da ke yaki da korona da kungiyar gwamnoni, na bayar da umarnin sassauta matakan kulle a Abuja da Legas da Ogun daga ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2020."
"Sai dai wannan sassauci bai shafi Jihar Kano ba."
"Game da Kano, na bayar da umarnin sanya dokar hana fita tsawon mako biyu da za ta fara aiki nan take. Gwamnatin Tarayya za ta bayar da dukkanin agajin da ake bukata na kayan aiki da kuma tallafi ga mutane domin taimaka wa jihar wurin yaki da annobar korona."
"Burinmu shi ne mu samar da tsari da zai tabbatar da cewa tattalin arzikinmu ya ci gaba da aiki a yayin da a hannu guda kuma za ku ci gaba da daukar tsauraran matakai kan yaki da annobar cutar korona.""Wadannan matakai irinsu ne shugabannin kasashe suka dauka a fading duniya."
"Sai dai bayan wannan sassauci za a sanya tsauraran matakai na tabbatar da yin gwaji da bin sawu, yayin da harkokin kasuwanci da na tattalin arziki kuma za su farfado."
"Za a ba da damar shiga da fita da kayayyakin bukatu tsakanin jihohi.""Za mu tabbatar da cewa ana amfani da takunkumin rufe fuska a cikin taron jama'a tare da tabbatar da ana bin dokar bayar da tazara."
"Amma dokokin hana taron addini da na shakatawa na nan za su ci gaba da aiki. Ana son gwamnatocin jihohi da kungiyoyi su dinga samar da takunkumin rufe fuska ga 'yan kasa."
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds