Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta Najeriya ta kaddammar da bincike mai zurfi, bayan bankado zargin da ake yi wa wasu tsofaffin shugabanin kamfanin mai na kasar NNPC.
Wadannan tsofaffin shugabanin kamfanin albarkatun man fetur din na Najeriya NNPC dai, na fuskantar zargin cin-hancin ne makwani kalilan bayan sallamarsu daga aiki. An dai kai ga gano Naira bilyan 80 a asusun daya daga cikin jami’an da ake bincike kan zargin karkatar da kudi dalar Amurka bilyan biyu da miliyan 900. Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa da yi wa TAttalin Arzikin Kasa Zagon Kasa ta Najeriyar EFCC, ta baza komarta ne a kan mutane 14 wadanda dukkansu tsofaffin manyan jami’an kamfanin na NNPC ne bayan da aka zarge su da sama da fadi da bilyoyin kudi da aka ba su amana a lokacin da suke jan ragamar kamafanin. Kama daga tsohon shugaban kamfanin na NNPC zuwa shugabanin wasu sassa na musamman na matatun man fetur din Najeriyar da aka kashewa dalar Amurka bilyan biyu da miliyan 900, amma kuma ana ta gyaransu na tsawon shekaru masu yawa. Ana zargin dai an mayara da kamfanin man wata lalita ta cin-hanci da rashawa.
#b#Tun daga 1999 da Najeriyar ta sake komawa kan mulkin dimukuradiyya, kamfanin na NNPCL na kasar ya zama wata kafar da ake zargin tafka gagarumar satar da ke rugurguza al’ummar kasar. Koda a 2014 sai da gwamnan babban bankin Najeriyar na wancan lokaci kana sarkin Kano na 16 a yanzu Muhammadu Sanusu na II ya bankado zargin karkatara da dalar Amurka biliyan 20 na man fetur, abin da ya janyo aka dakatar da shi. Tuni dai tsohon shugaban kamfanin albarkatun man a Najeriya Mele Kyari wanda ke cikin mutanen 14 da ke fuskantar bincike ya bayyana cewa, a shirye yake da ya kare kansa daga duk wani zargi da ake masa. Ana dai nuna damuwa, a kan yadda ake barin sai an tafka barna an sallami jami’ai sannan a fara bincike.A cewar Dakta Umar Yakubu na Cibiyar Tsage Gaskiya da Adalci ya bayyana cewa, akwai bukatar a yi wa kamfanin na NNPCL wankan tsarki. Duk da girman wannan zargi akwai tsoron amfani da tsarin nan na wadanda aka samu da laifi za su bayar da wani kaso na abin da suka sata a barsu su yi tafiyarsu, lamarin da kwarrau ke bayyana cewa yana kara janyo wasu su aikata laifin maimakon zama darasi.
EFCC: Binciken tsofaffin shugabannin NNPC – dw.com
