Asalin hoton, NAHCON
Hukumar Alhazan Najeriya wato NAHCON ta ce ta kammala kwashe maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki, a daidai lokacin da hukumomin Saudiyya suka sanar da rufe filin jirgin Sarki Abdul'aziz da ke Jeddah.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, hukumar ta ce "Jirgin karshe na maniyyata zuwa aikin Hajji na shekarar 2024 zai tashi daga Abuja da sanyin safiyar ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024, inda zai nufi Madina."
Ana dai sa ran cewa jirgin zai ɗauki kimanin alhazai 211 daga Zamfara da Sokoto da Kebbi da Bauchi da Abuja da kuma jNeja, tare da rukunin karshe na jami’an aikin Hajji a cikin jirgin na FlyNas.
Hakan ne ya kawo ƙarshen "jigilar alhazai na bana zuwa Saudiyya inda Aero Contractors za su kammala jigilar Alhazai masu zaman kansu da karfe 2:00 na rana a yau." In ji hukumar.
Ana kuma sa ran kamfanin Aero Contractors masu jigilar maniyyata masu zaman kansu su kammala jigilar maniyyatan da karfe 2 na rana a ranar 10 ga watan Yunin 2024, kafin rufe filayen jiragen sama na Jeddah da Madina don gudanar da ayyukan jigilar alhazai masu shigowa.
Dangane da kuma shirin komawa Najeriya bayan aikin Hajjin na bana, hukumar ta ce za ta fara ne a ranar 22 ga Yuni, 2024, bisa tsarin waɗanda suka fara shiga su ne za su fara komawa.
Ranar Litinin din nan ce ranar da hukumomin ƙasar Saudiyya suka tsayar mastayin ranar cikar wa'adin kammala jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga kowace kusurwa ta duniya.
Da karfe 12 na tsakar daren yau Litinin agogon Saudiyya ne hukumomin na Saudiyya suka ce za su rufe filayen jiragen saman ƙasar 6 ga saukar duk wani jirgin da ya dauko maniyyata daga kowace kasa ta duniya.
Hakan ya sa ƙasashe musamman waɗan da ke da adadi mafi yawa na maniyyatan da ke rige-rigen ganin sun kammala jigilar maniyyatansu kafin cikar wa’adin.
Filayen jiragen su ne waɗan da aka keɓe domin jigilar maniyyatan na bana da ke biranen Riyadh, da Jiddah, da Madina, da Dammam, da Taif, da kuma Yanbu’u.
Sai dai hukumomin sun ce rufewar ba za ta shafi jiragen da suka ɗauko fasinjojin da za su shiga ƙasar domin kasuwanci, da yawon bude ido, da ziyaratar ƴan uwa da dukkan wata lalura da ba ta shafi aikin Hajji ba.
Yanzu haka dai ƙasashe duniya na ta fadin tashin ganin sun kammala jigilar maniyyatansu kafin cikar wannan wa’adin da hukumomin saudiyyan suka ɗibar musu.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Hajj 2024: Yau Saudiyya ke rufe saukar Alhazai – BBC
