Hukumar FCTA ta lalata babura 601 da aka kama a Abuja bayan dokar hana acaba – Legit.ng

Global site navigation
Na gargajiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar DRTS ta FCTA ta lalata babura 601 da aka kama bisa laifin zirga-zirga a wuraren da aka hana a babban birnin tarayya Abuja.
Sakataren ma’aikatar sufuri ta FCTA, Elechi Chinedum, ya jagoranci jami’an gwamnati wajen gudanar da aikin a wani wuri da aka tanada.
Kara karanta wannan
‘Dole Tinubu ya zarce,’ Minista ya bukaci ‘yan APC su tashi tsaye kan 2027
Jaridar Vanguard ta rahoto Elechi ya bayyana cewa an rukurkushe baburan ne bisa dokar da FCTA ta gabatar a ranar 1 ga Janairu, 2023, karkashin tsohon minista, Muhammad Bello.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Elechi Chinedum ya ce doka ce ta hana amfani da babura a wasu yankuna na Abuja, kuma an tanadi hukunci ga masu karya dokar.
Ya ce tun farko an kafa dokar ne domin kyautata tsarin birnin Abuja, amma yanzu ta koma mai yaki da matsalar tsaro da aikata laifuka.
Daraktan DRTS, Abdulateef Bello, ya bayyana cewa aikin kame babura da kuma lalata su zai taimaka wajen dakile cin zarafin doka da kuma kare lafiyar jama’a.
Kara karanta wannan
Abin fashewa da ake zargin bam ne ya tarwatse a Borno, sama da mutane 25 sun mutu
Ya tuna cewa haramcin tuka babura a birnin Abuja ya fara tun a shekarar 2006 bisa dokar hana amfani da baburan domin sana'ar 'acaba.'
Jaridar Daily Trust ta rahoto, Abdulateef Bello ya ce babura suna taimaka wa masu aikata laifi, kuma hakan ya jefa al’ummar birnin Abuja cikin barazanar tsaro.
Shugaban DRTS ya ce wadannan babura 601 da aka lalata su ne rukunin farko da aka lalata a shekarar 2025, kuma hakan na nuna tsayin daka na FCTA wajen tabbatar da doka.
Kara karanta wannan
Natasha ta barowa Akpabio aiki a wasikar ‘ba da hakuri’ da ta rubuta masa
Ya gargadi masu sana'ar acaba da su kauracewa Abuja, yana mai cewa gwamnati ba za ta daina daukar mataki mai tsauri ba idan ta kama baburansu.
Abdulateef Bello ya jaddada cewa DRTS za ta ci gaba da sa ido a titunan Abuja don tabbatar da cewa doka tana aiki yadda ya kamata.
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar FCTA ta lalata fiye da babura 1,700 da aka kama, yayin aiwatar da haramcin aikin 'yan acaba (Okada) a Abuja.
Daraktan hukumar kula da zirga-zirga ta FCTA, Dr. Abdulateef Bello, ya ce murkushe baburan wani mataki ne na gargadi ga masu karya doka da oda.
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta bayyana cewa an kama baburan ne sakamakon aikata miyagun laifuka da ake yi ta amfani da su a babban birnin kasar.
Asali: Legit.ng
Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma’aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana’antar fina-finai da dab’i.
Mun zaba maka wannan





Duba karin labarai a nan

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds