Asalin hoton, @NigAirForce
An yi jana'izar sojan sama na Najeriya da ya rasu a hatsarin jirgin sama a unguwar Katampe a Abuja.
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce an binne sojan ne a makabartar unguwar Gudu da ke Abuja bisa tsarin addinin Islama.
Sojan mai suna Squadron Leader Bello Mohamed Baba-Ari, ya rasu ne ranar juma'a sakamakon hatsarin jirgin sama yayin atisayen shire-shireyen bukukuwan ranar samun 'yancin Najeriya wanda za a yi ranar Litinin mai zuwa.
A cikin wani sakon twitter, kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Ibukunle Daramola ya bayyana marigayin a matsayin kamilin mutum mai kishin kasa kuma gwarzo a fagen yaki da ta'addanci.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Babu karin bayanai
Babban hafsan sojin sama na Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar, wanda ya mika sakon ta'aziyarsa ga dangin mamacin a twitter ya ce matashin sojan yana cikin sojojin sama da suka kware a harakar jirgin sama.
Jirage biyu ne suka fadi bayan da suka gogi juna.
Asalin hoton, Family
Wakilin BBC Abdou Halilou da abun ya faru a gabansa, ya ce ya ga faduwar jiragen inda kuma daya ya kama da wuta nan take.
Ya ce jirage uku ne ke tafiya a jere, inda kuma ya ga faduwar daya a tsaunin Katampe.
Ya kuma ce kafin jirgin ya fado, daya daga cikin mutanen da ke cikinsa ya diro da lemar jirgi sannan jirgin ya kama da wuta.
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce matuka uku sun fita daga cikin jiragen ta hanyar amfani da lema.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a wani sakon Twitter ta hanyar kakakinsa Malam Garba Shehu, ya jajantawa rundunar sojin sama ta Najeriya na rashin daya daga cikin sojanta tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga sauran sojojin da suka ji rauni.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Babu karin bayanai
A cikin wata sanarwa, Kakakin rundunar sojin saman Najeriya ya ce hafsan hafsoshin sojin sama na kasar Air Marshall Sadiq Abubakar ya kafa wani kwamitin da aka dorawa alhakin gudanar da bincike kan gano musababbin abin da ya janyo faduwar jiragen saman.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Kun san sojan da ya rasu a hatsarin jirgi a Abuja? – BBC
