A ƙarshen wannan makon ne musayar yawu tsakanin ministan Abuja Nyesom Wike da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ta sake ɓarkewa a karo na biyu da masana kimiyyar siyasa ke alaƙantawa da shugabancin Najeriya a 2027.
Irin wannan musayar zafafan kalaman sun faru tsakanin mutanen guda biyu a makonni biyu da suka gabata.
Bala Muhammad dai shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, inda shi kuma Nyesom Wike ya kasance mai goyon bayan shugaban jam'iyyar PDP da ake taƙaddama a kansa, Umar Damagum.
Bala Muhammad ya yi ministan Abuja a lokacin Goodluck Jonathan, inda shi kuma Nyesom Wike yake ministan Abujar mai ci.
A ranar Asabar ɗin nan ne gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar PDP na Najeriya, Bala Muhammad ya bayyana ministan Abuja, Nyesom Wike da "mutumin da ya daɗe yana cin amana kuma barazana ga jam'iyyar hamayya ta PDP", inda ya buaci da ya yi murabus daga jam'iyyar ta PDP domin samun damar zama an jam'iyyar APC mai mulki cikakken.
Bala Muhammad ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin ƴanjaridu, Mukhtar Giɗaɗo ya fitar, inda gwamnan ya caccaki Wike bisa zargin sa da "rarraba kan ƴan PDP da kuma cin amanar jam'iyyar."
Giɗaɗo ya ƙara da cewa "Wike ya ci amanar mutane irin su Peter Odili da sanata John Mbata da tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi," da kusan duk "tsoffin shugabannin jam'iyyar PDP."
Dangane kuma da kasancewar Wike a matsayin ministan Abuja, Giɗaɗo ya ce "ba zai yiwu a haɗa irin nasarorin da Bala Muhamamd ya samu a Abuja a matsayin ministanta ba da na Wike wanda ya fi mayar da hankali wajen rushe-rushe da ƙwace filayen mutane."
To sai dai tsohon gwamnan jihar Rivers ɗin kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ya mayar da martani ranar Lahadi.
A wata tattaunawa da babban mai taimaka masa kan harkokin ƴanjaridu, Lere Olayinka ya yi da jaridar The Punch ranar Lahadi, Wike ya ce "gazawar shugabanci" ne matsalar jam'iyyar PDP."
"Mutum ne kda ya saba gazawa a duk inda ya tsinci kansa sannan kuma maciyin amana ne."
"Mun faɗa masa gaskiya kuma yanzu ya rage nasa ya saurari gaskiyar. Ya kamata ya daina mafarkin neman takarar shugaban ƙasa a 2027," in ji Olayinka.
Olayinka ya ƙara da cewa uabngidansa (Nyeson Wike) har yanzu ba ɗan jam'iyyar APC ba ne saboda ya karɓi muƙamin minista, inda ya ce "Wike nan nan daram a jam'iyyar PDP."
Malam Kabiru Sufi- masanin kimiyyar siyasa a Najeriya ya shaida wa BBC cewa "wannan rikicin ba sabo ba ne illa dai ace yanayi ne ya ƙara sabunta shi".
"Dama dai za a ci gaba da samun haka kasancewar wasu jigajigan jam'iyyar sun gaji da cigaba da zaman Wike a jam'iyyar ta PDP domin a tunaninsu shi ne mutumin da ya hana ruwa gudu a jam'iyyar kasancewar shi bai fita ba kuma ya hana ta zaman lafiya." In ji Malam Kabiru.
Ya ƙara da cewa mutanen bitu wato Nyesom Wike da Bala Muhammad "dukkansu na shirin zaɓen 2027, inda ya shi Bala Muhammad ke son tsayawa takara, shi kuma Wike ke nuna hamayya da hakan.
Saboda haka za su ci gaba da musayar yawu na siyasa har zuwa lokacin da za a samu mafita a jam'iyyar PDP a matakin ƙasa da ma jihar Rivers." In ji Malam Kabiru Sufi.
Ɗaya daga cikin ƴan kwamitin amintattu kuma dattijo a babbar jam'iyyar hammaya ta Najeriya, PDP, Ambassada Aminu Wali, ya zargi jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya da cewa ita ke rura wutar da ta hana jam'iyyarsu zama lafiya, ake ta samun rikici a cikinta.
A hirarsa da BBC, Ambassada Wali wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙirƙiro jam'iyyar ta PDP ya ce sun tabbata ba haka kawai jam'iyyar ta samu kanta a wannan hali ba da hannun APC ba. ''Ka tabbata cewa tilas APC suna da ruwa da tsaki a cikin rgingimun da ke faruwa a cikin wasu jam'iyyu a Najeriya.
''Kwanaki kwamitin zartarwar ba ta dare gida biyu ba sai daga baya aka zo aka yi musu faci da ƙyar suka gyaru,'' in ji shi.
Ya ce ba abu ne da daman zai fito fili ba cewa APC ta fito ta nuna cewa tana da hannu a rikicin ko kuma ta bayyana cewa ga abin da take yi.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Me ke janyo yawan musayar yawu tsakanin Wike da Bala Muhammad? – BBC
