Me ya sa aka rufe filin jirgin saman Abuja? – BBC

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) ta ce an bude filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan rufe shi da aka yi na wasu sa'o'i sakamakon wani hatsari.
A wata sanarwar da ta fitar a shafinta na Twitter, hukumar ta ce an rufe wani sashe na titin filin jirgin saman Abuja din ne da karfe 11 na daren Laraba bayan wani jirgi ya kauce daga kan titin jirgi a lokacin da yake sauka.
Matsalar ta sa an dakatar da sauka da kuma tashin jirge a filin.
An ringa karkatar da wasu jiragen zuwa wasu filayen jiragen sama kamar a kasar har ma da jamuhuriyar Benin.
Sai dai kuma sanarwar ta ce hukumar ta sake bude titin jrgin saman domin sauka da tashin jirage.
End of Wanda aka fi karantawa
Ta kuma tabbatar wa kamfanonin jiragen sama da fasinjoji cewar za su iya amfani da filin jirgin saman ba tare da wata matsala ba.
Wasu da suke aikin a filin jirgin na Abuja sun tabbatar wa BBC cewa tuni jirage suka fara sauka a filin da safiyar Alhamis, bayan tsaikon da aka samu.
Rufe filin jirgin na sa'o'i da dama a babban birnnin kasar ya sa wasu suna sanya alamar tambaya kan rashin kayan aikin da za a iy janye jirgin da ya kauce ba tare da an shafe sa'o'i ba.
A bara ne dai hukumomin Najeriya suka rufe filin jirgin saman na Abuja na wasu makwanni, domin gudanar da wani gyara a filin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Babu karin bayanai
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds