Asalin hoton, Google
Lauyoyin yaran nan da gwamnatin Nijeriya ta gurfanar a gaban kotu kan zanga-zangar neman a kawo ƙarshen rashin ingantaccen shugabanci a watan Agusta, sun ce za su koma gaban alƙali cikin makon gobe don neman sassauci game da sharuɗɗan belin da aka ba su.
Lauyoyin dai sun ce sharudan da kotu ta sanya wa wadanda aka gurfanar din sun yi tsauri, ba za su iya cika su ba, kasancewar da dama daga cikinsu basu da wani da ke aiki a Abuja, musamman ma wadan suke zo daga Kano.
Daya daga cikin lauyoyin Barista Hamza Nudu Dantani, ya ce ‘Idan ka gansu sai ka tausaya musu, akwai wata uwa da ta ce da ni, ita bata taɓa zuwa Abuja ba, sai wannan karon, nine ma na ba ta kudi ta koma, irin wadannan mutanen kake cewar za su cika maka wadannan sharudan?’
Wani sharadin a cewar baristan shine dole sai kowanne daga cikin yaran ya samu wani ma'aikacin gwamnati mai mukamin darakta da zai tsaya masa, da kuma bayar da belin Naira miliyan goma.
Tuni dai wasu jagororin adawa a ƙasar kamar Atiku Abubakar da Peter Obi suka fito suka yi tur da tsare yaran tsawon lokaci da kuma azabtar da su.
A jiya Juma’a ne babbar kotun tarayya a Abuja, ta ba da belin waɗanda ake ƙarar su 118 bayan kama su a jihohin Kano da Kaduna bisa tuhume-tuhumen da suka haɗar da cin amanar ƙasa da tunzura bore soja a lokacin zanga-zanga.
Hamza Nuhu Ɗantani, ya ce wasu ma a cikin gida, aka kama su, wasu ko zanga-zanagar basu fita ba, akwai wani ma da aiken shi aka yi ya siyo wa ƙanwarsa magani bata da lafiya aka kama shi, toh shi din ma bashi da lafiya, yan uwansu da suka zo in kagansu sai ka tausaya musu suna ta kuka” inji shi.
Haka kuma Bar. Hamza Nuhu Ɗantani ya ce yaran da suka faɗi a kotu sakamakon jigatar da suka yi, da rashin abinci mai gina jiki, saboda kasancewar su wattanin uku a rufe, wanda hakan ya janyo wasu daga cikin mutum 5 zuwa shida da suka fadi a kotun, wanda alƙalin ya ce ba zai iya zaman kotun ba. Amma an kai su asibiti don samun kulawar likita.
Sai dai ya ce ranar litinin za su shigar da wata bukata gaban kotun don ganin an sassauta sharudan belin da aka bayar, wanda kuma suke fatan ganin cewar kotun za ta dubi halin da yaran suke ciki ta yi abun da ya kamata.
Ya kara da cewa kotu ta aike da manya daga cikin wadan aka kama din zuwa kurkukun Kuje, yayin da kanan yaran kuma aka mayar da su gidan kula da yara, da ke Abuja.
Sai dai shi ma ministan Shari’a na Najeriya Prince Lateef Fagbemi (SAN) a wata sanarwa da ya fitar a cikin daren ya buƙaci runduanr yan sandan Najeriya da ta gabatar masa da kundin shari’ar mutanen a yau Asabar 2 ga watan Nuwambar, 2024.
Haka kuma ministan Shari’ar na Najeriya ya ce ta mika kwafin kundin ga daraktan gabatar da ƙara na ma'aikatar shari'ar shi ma a goben.
Sannan kuma ya umarci daraktan gabatar da ƙara, da ya tuntubi kotu ta saka ranar da za a dawo don ci gaba da sauraron shar’ar a kusa.
An kama waɗanda ake zargin ne a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a faɗin Najeriya tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
An kama su ne a garuruwan Kano, da Katsina, da Gombe, da Abuja, da Jos, da Kaduna.
Daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi musu akwai cewa "sanya wa tare da ɗaga tutar Rasha, suna rera waƙoƙin juyin juya-hali tare da kira ga Rasha ta kawo ɗauki a Najeriya".
A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da mutum 10 a gaban kotu, waɗanda ta zarga da jagorantar zanga-zangar. Daga baya kotun ta ba da belinsu kan naira miliyan 10 kowannensu, yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar tasu.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Ministan shari'ar Najeriya ya buƙaci ƴan sanda su mayar da batun yaran da aka gurfanar ofishinsa – BBC
