Yayin da a wannan rana 1 ga watan Oktobar 2024, ake bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, wasu ƙungiyoyin fararen hula a ƙasar sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa domin nuna adawa da manufofin gwamnatin shugaba Tinubu kan tattalin arziki da ƙarin farashin man fetur wanda sune jigo wajen jefa 'yan ƙasar cikin halin matsin rayuwa.
Wasu shugabannin kungiyoyin fararen hula a Najeriyar, sun ce za su ci gaba da matsawa gwamnati lamba a kan irin manufofin da ta ɓullo da su wanda suka ce sun sanya al'ummar Najeriyar cikin halin ni-'ya-su.
'Yan Najeriya da dama dai sun ce za su fito don bin sahun zanga-zangar domin nuna ɓacin rai saboda gazawar gwamnati na cika alkawuran da ta ɗauka.
To sai dai kuma a ɓangare guda rundunar 'yan sandar Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja ta sanar da cewa babu wani bayani da ta samu kan cewa za a gudanar da zanga-zanga, kuma ta ɗauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Muƙaddashin kwamishinan 'yan sanda na babban birnin tarayar Abuja, DCP Isiyaku Sharu, ya shaida wa BBC cewa, kullum a shirye suke wajen tabbatar da doka da oda.
Ya ce, "A kodayaushe bama barin ko-ta-kwana musamman idan muka samu wani labari na gudanar da wata tarzoma ko zanga-zanga ko dai yin wani abu da zai haifar da wata matsala ga tsaron kasa, to bama wasa muna yin duk mai yiwuwa wajen kare rayukan da dukiyoyin mutane".
DCP Isiyaku, ya ce hakkinsu ne don haka a ko yaushe cikin shiri suke.
"Batun za a gudanar da zanga-zanga a ranar bikin saun ‘yancin kai mu dai ba samu labarin haka ba don ba a sanar damu ba a jarida muka gani, to don haka mu koda zanga-zanga ko ba zanga-zanga, mu hakkinmu ne mu sauke nauyin da aka rataya mana na tabbatar da zaman lafiya".
A farkon watan Augustan 2024, an gudanar da zanga-zangar gama gari a Najeriya inda al'ummar kasar suka fita don jawo hankalin gwamnati game da karuwar matsin rayuwa da jama'ar kasar da dama ke fuskanta.
To sai dai kuma zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tarzoma a wasu jihohin Najeriyar bayan wasu matasa sun fara afka wa wuraren ajiye abinci suna wawashewa.
Hakan ya haifar da arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro.
Zanga-zangar ta watan Augusta, ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Nigeria @64: Jami'an tsaro na cikin shirin ko-ta-kwana a Abuja – BBC
