Nigeria: Zanga-zangar 'yan tasi ta tsayar da al'amura a Abuja – BBC

Wata zanga-zanga da direbobin tasi suka yi ta tsayar da al'amura a Abuja, babban birnin Najeriya, inda aka kona tayoyi tare da hada cunkoson motoci a sassan birnin da dama.
Tarzomar ta samo asali ne bayan da direbobin suka zargi jami'an rundunar hadin gwiwa ta birnin da kisan daya daga cikinsu.
Kawo yanzu dai jami'an rundunar ba su ce komai ba kan wannan zargi. Kuma yunkurin BBC na ji daga bakin jami'an ya ci tura.
Wannan batu ne ya kai ga rufe babbar hanyar da ta hada sassan birnin da babbar kasuwar Wuse, abin da ya sa birnin ya cunkushe.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan birnin ya shaida wa BBC cewa za su fitar da sanarwa nan gaba kan lamarin.
End of Wanda aka fi karantawa
Shi kuwa wani dan kusuwa da ke harkokinsa a kasuwar ta Wuse ya shai da wa BBC cewa sun shiga fargaba saboda tsoron kada wani abu ya shafi dukiyarsu.
Ya kara da cewa 'yan kasuwa da dama ba za su yi ciniki kamar yadda suka saba ba, saboda tsaikon da aka samu.
Babu tabbas kan mataki na gaba da masu zanga-zangar za su dauka nan gaba.
A yanzu rahotanni sun nuna cewa al'amura sun fara lafawa.
An dade ana samun sabani tsakanin jami'an wannan runduna da kuma masu motocin haya, inda masu motocin ke zarginsu da ci musu zarafi.
Sai dai jami'an rundunar sun sha musanta wannan zargi.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds