NLC da TUC: Yadda ƴan ƙwadago suka tsayar da ayyuka cak a Najeriya – BBC

Asalin hoton, Getty Images
Litinin ce ranar farko ta yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka shiga a Najeriya bayan gaza cimma matsaya kan ƙarancin albashi.
A ranar ta Litinin an ga yadda ƴan ƙungiyar suka riƙa zagayawa suna rufe ma’aikatu da hukumomi, ba kawai na gwamnati ba, har ma da bankuna.
A Abuja babban binrin Najeriya ƴan ƙwadagon sun rufe Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), da Majalisar dokokin Najeriya, da sakatariyar tarayyar ƙasar da ginin Bankin masana’antu (BOI) da ma wasu da dama.
Haka nan wasu daga cikin manyan hanyoyin babban birnin ƙasar sun kasance fayau, kasancewar babu zirga-zirgar ma’aikata masu zuwa wuraren aiki.
A birnin Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar ƴan ƙwadago sun rufe sakatariyar Audu Baƙo da ke birnin da kuma wasu bankuna.
Haka labarin yake a Legas, cibiyar kasuwanci ta ƙasar ta Najeriya, inda ƴan ƙwadago suka dakatar da sauka da tashin jaragen sama.
Kamfanin Ibom Air ya fitar da wata sanrwa da ke cewa “Muna baƙin cikin sanar da ku cewa mun kasa gudanar da zirga-zirga zuwa wuraren da muka saba sanadiyyar yajin aikin ƴan ƙwadago da ke gudana a fadin ƙasa”.
Kamfanin raba wutar lantarki na Najeriya TCN ya fitar da wata sanrwa da safiyar ranar Litinin ɗauke da sa hannun shugaban sashen harka da jam’a, Ndidi Mbah, yana sanar da katsewar lantarki a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta ce “Muna sanar da al’umma cewa Ƙungiyar ƙwadago ta kashe hanyar rarraba lantarki ta ƙasa, lamarin da ya haifar da katsewar lantarki a faɗin ƙasa.
“Katsewar lantarki ta faru ne da ƙarfe 2:19 na daren wannan rana ta uku ga watan Yuni, 2024”.
Cibiyoyin samar da wutar lantarkin da aka rufe su ne na Benin, da Ganmo, Ayede, Olorunsogo, Akangba da Osogbo.
Haka nan lamarin ya shafi tashar samar da lantarki ta Jebba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Babu karin bayanai
Su wane suka shiga yajin aikin?
Ga alama a wannan karo ƙungiyoyi da dama sun yi biyayya ga umarnin ƙungiyar ƙwadagon wajen shiga yajin aikin.
Cikin ƙungiyoyin da suka shiga yajin aikin sun haɗa da:
Ƙungiyar ma’aikatan jiragen ƙasa ta Najeriya
Ƙungiyar ma’aikatan lantarki ta ƙasa
Ƙungiyar likitoci da masu aikin lafiya ta Najeriya
Ƙungiyar ƴanjarida ta Najeriya
Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da gasa ta Najeriya
Ƙungiyar ma’aikatan ɓangaren shari’a ta Najeriya
Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatun hukumomin gwamnati
Ƙungiyar ƙwararrun ma’aikatan harkokin jiragen sama ta Najeriya
Ƙungiyar injiniyoyin gine-gine da masu haɗa kayan ɗaki ta Najeriya
Akwai yiyuwar ayyukan tattalin arziki a Najeriya su tsaya cik sanadin yajin aikin da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC suka fara.
Kokarin da shugabannin Majalisar dokokin kasar suka yi domin sasanta bangarorin ya ci-tura.
Bayan ganawar sa’o’i hudu da shugabannin Majalisar dokokin kasar da yammacin ranar Lahadi a Abuja, an kasa samun matsaya, inda shugabannin kungiyar kwadagon suka "babu gudu babu ja da baya" game da yajin aikin gama gari da aka shirya ya fara ranar Litinin 3 ga watan Yuni, 2024.
Sai dai shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ya ce za su tuntubi sauran ressansu a kan kiran da shugabannin Majalisar suka yi musu a kan su janye yajin aikin:
“A yanzu ba mu da hurumin janye yajin aikin, yajin aikin zai fara ne yayin da mu mika rokon da shugabannin Majalisar dokokin kasar suka yi ga ressanmu daban-daban, game da kiran da suka yi a kan mu janye yajin aikin” inji shi.
Tun da farko, Osifo, shugaban kungiyar kwadago (TUC); da takwaransa na kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero; sun gana da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas. a Abuja.
Kungiyoyin kwadagon sun kira yajin aikin ne sakamakon rashin cimma matsaya a tattaunwar da bangarorin biyu ke yi da gwamnatin kasar kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Kwamared Ibrahim Abubakar Walama , wanda mamba ne a kwamitin zatarwa na kungiyar ta NLC ya shaida wa BBC cewa sun dauki wannan mataki ne saboda tura ta kai bango:
"Duk mun ce za mu shiga yajin aikin gama gari saboda tura ta kai bango, gwamnati ba ta dauki maganar albashi da muhimanci ba’.
''Yau gwamnati ta ce dubu 60 za a bayar, shin me mutum zai saya da dubu sistin?'' in ji shi.
Kwamared Walama ya ce janye tallafin man fetur da na kudin wutar lantarki da gwamnatin kasar ta yi a baya bayan sun kara jefa mutane cikin hali na kaka-ni-kayi
Rahotanni sun ce shugabbanin majalisar dokokin kasar sun shiga tsakani domin kokarin ganin cewa yajin aikin bai gudana ba.
Kungiyoyin kwadagon na NLC da TUC sun ce suna son gwamnati ta yi 'abinda ya dace' a kan albashi mafi karanci na ma’aikata domin rage musu radadin tsadar rayuwa.
Gwamnatin Najeriya ta yi wa kungiyoyin kwadogon tayin naira 60,000 a matsayin albashi mafi karanci sai dai kungiyoyin kwadagon sun yi watsi da tayin inda suka bukaci naira 494,000.
Kungiyoyin sun kuma bukaci gwamnati ta soke karin da ta yi wa farashin wutar lantarkin kasar.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds