Shin an samar da tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna? – BBC

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da samun rahotanni da ke cin karo da juna kan ikirarin da jami'an tsaro suke yi cewa sun tabbatar da tsaro a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Babbar hanyar ta yi kaurin suna wajen sace-sacen mutanen don neman kudin fansa, inda mahara suke cin karensu babu babbaka.
Kabiru Adamu, wani masani kan harkokin tsaro a kasar, ya ce an sace kimanin mutum 200 a babbar hanyar a watanni hudu na farkon wannan shekarar.
Amma akwai wadanda suke ganin adadin ya wuce hakan.
Galibin matafiya da ke zirga-zirga a hanyar yanzu suna amfani ne da jirgin kasa, maimakon motoci da suka saba amfani da su a baya.
A makon da ya wuce ne jami'an tsaro a kasar suka ce sun tabbatar da tsaro a wannan babbar hanyar, kuma jama'a za su iya ci gaba da amfani da ita ba tare da fargaba ba.
Wakilinmu Mukhtari Adamu Bawa ya kai ziyara babbar tashar mota ta unguwar Jabi a Abuja don jin ta bakin wasu direbobi kan ikirarin na jami'an tsaron.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds