Asalin hoton, PIERRE FAVENNEC
A duk lokacin da aka yi maganar birnin tarayya Abuja abin da ke fara zuwa zukatan al'umma shi ne nan ne tudun mun-tsira ga duk wanda jiharsa ko kuma garinsa yake fama da matsalar tsaro.
To sai dai alamu da abubuwan da ke faruwa na nuni da cewa al'amarin ba haka yake ba domin ita kanta birnin tarayyar ba ta tsira ba.
A wannan labari, wakilin BBC, Usman Minjibir ya duba mana matsalar tsaron da kowacce daga kananan hukumomin birnin tarayyar guda shida:
Abaji ce karamar hukumar birnin tarayya mai iyaka da jihohin Kogi da Nassarawa masu fama da matsalar daga kudanci.
Duk da cewa yanzu haka al'amura sun tsahirta a karamar hukumar, amma a baya karamar hukumar ta shiga hannu masu garkuwa da mutane, inda 'yan bindiga kan shiga garin su kwashi mutanen da ransu yake so.
Wani abun da ke nuna girman rashin tsaron karamar hukumar shi ne yadda garin Abaji yake a bushe sakamakon rashin zaman 'yan asalin karamar hukumar a garuruwansu saboda tsoron masu garkuwa da jama'a.
"Ya kamata a ce Abaji ta fi haka cikar jama'a saboda tsohon gari ne mai matukar tarihi amma dubi yadda garin yake. Babu wanda zai zauna 'yan bindiga su zo su sace shi", in ji wani mazaunin Abaji.
Sakamakon hada hannu da karfe da sarakunan gargajiya da jami'an tsaro suka yi ya sa aka kafa kungiyar 'yan banga domin yin aiki tare da jami'an tsaro, wani abu da ya bai wa mutanen garin samun damar kama masu kwarmata bayani da ke tsegunta wa masu garkuwa a kan masu hannu da shuni.
Al'amarin dai ya fi kamari a yankunan da ke kewaye da garin na Abaji.
Kamar Abaji, ita ma karamar hukumar Kwali na da tata matsalar tsaron duk da cewa kwaryar garin na Kwali bai taba fuskantar hare-haren masu garkuwa da jama'a ba – Abun ya fi kamari a kewayen karamar hukumar.
Garin Yangoje da ke makwabtaka da Kwali shi ne wanda ya fi kowanne gari a karamar hukumar fuskantar matsalar masu garkuwa da mutane.
Ko a makonni biyu da suka gabata, sai da aka sace babban limamin garin inda ya kwashe fiye da mako guda a hannunsu har zuwa lokacin da aka kammala biyan kudin fansa.
"Sun kira mu sun ce mu aiaka musu da naira miliyan biyu da rabi da nama da madara da abinci da kuma katin waya. Da aka kai musu sai su ka rike wanda ya kai kudin suka saki daya daga cikin yaran limamin da aka sata tare bayan da miciji ya sare shi."
Kafin nan kuma sai da masu garkuwar suka yi awon gaba da wani fasto wanda bayan an sake shi ya bar yankin.
Baya ga faston ma mutane da dama sun bar yankin sakamakon fargabar abin da ka iya samun su a kowane dare.
Gwagwalada
A duk lokacin da aka yi amaganar Gwagwalada wadda ita ce karamar hukuma ma fi girma a Abuja, abin da ke fara zuwa zukatan mutane shi ne harin da aka kai rukunin gidajen ma'aikatan jami'ar Abuja, inda aka yi awon gaba da mutum shida, ciki har da farfesoshi guda biyu da 'ya'yansu.
A ranar Talata ta 2 ga watan Nuwamba ne dai 'yan bindigar fiye da 50 suka far wa rukunin inda suka rinka bi gida-gida suna tsintar mutane.
"Da suka zo sai suka raba kansu wuri-wuri domin yin kwantan bauna koda wani zai kawo dauki. Sannan sai suka yi amfani da sanduna suka farfasa kwayayen wutar lantarki domin su sanya wurin a duhu. Kuma da yin hakan sai kawai suka fara bude wuta. Saboda da tsabar harbi karnuka ma tsit suka yi", in ji wani wanda ya shaida faruwar al'amarin.
To sai dai bayan kwana uku, rundunar 'yan sanda Najeriya da ke birnin tarayya ta ce an ceto mutanen shida ba tare da biyan kudin fansa ba.
Ita ma Kuje babu wasu rahotanni ko bayanai da ke nuna an taba garkuwa da wani a cikin hedikwatar karamar hukumar. Sai dai akwai wasu wurare da shigarsu na da wuya ga mutumin da ke cikin garin Kuje sakamakon sansani da 'yan bindiga suka yi a dazukan.
Wani mazaunin Kuje ya shaida wa BBC cewa "gaskiya cikin garin Kuje babu matsala duk da dai muna zama ne cikin fargaba saboda tsakaninmu da su bai wuce kilomita bakwai zuwa takwas ba. Yanzu idan ka za ka kauyuka kamar Kabin Mango ko kuma Kwaku to fa kana cikin tararrabi. An sha dauke manoma da ke zuwa gona."
Wani wuri da ya yi kaurin suna a Kuje wajen satar mutane shi ne garin Pegi mai nisan kilomita 10 daga hedikwatar karamar hukumar Kuje. Kimanin watanni uku da suka gabata, garin na Pegi ya zama tamkar karkatacciyar kuka ga masu satar mutane inda suka yi ta yin garkuwa da jama'a har ma al'amarin ya kai ga kisa idan ba a biya kudin fansa ba.
"Gaskiya yanzu dai an samu zaman lafiya kasancewar a nan garin jami'an tsaro da 'yan banga na ta sanya ido da yin sintiri", in ji wani mazaunin garin Pegi.
Yanuz dai idan kana tafiya zuwa pegi za ka tsinkayi sansanonin jami'an tsaro sannan wasu na shawagi domin zama cikin shirin ko-ta-kwana.
Kuje ce karamar hukumar da ta fi kowacce girman kasa da dazuka kuma ita ce cibiyar noman birnin Abuja.
Bwari ce karamar hukumar birnin tarayya da ta yi iyaka da jihohin Kaduna da Naija masu fama da matsalar tsaro kuma lokaci zuwa lokaci a kan samu hare-haren masu garkuwa a yankunan Bwari.
Ita ma kamar sauran kananan hukomomin na Abuja, ba a taba samun hare-haren 'yan bindiga ko kuma masu garkuwa da jama'a ba a cikin garin Bwari.
Sai dai wasu garuruwa kamar Dikko da Tudun Fulani na cikin wadanda al'amarin ya fi yin kamari a ciki.
Dan taki ne kawai tsakanin garin na Bwari da Tudun Fulani kuma ga wanda bai sani ba zai iya cewa duk gari daya ne.
"A baya mun yi fama da masu garkuwa a nan garin inda kawai cikin dare za a zo a kwashi mutane. Yanzu dai in takaice maka bayani, mutane da dama sun sayar da gidajensu sun koma cikin gari. Sannan harkar saye da sayar da filaye ma ta ja baya", in ji wani mazaunin Tudun Fulani.
Sai dai ya kara da cewa "yanzu mun samu nasarar kawo karshen al'amarin sakamakon aiki da muka yi tare da jami'an tsaro da 'yan sintiri inda muka samu nasarar damke masu kwarmata bayanai da ke zaune a cikinmu."
Kusan duk ilahirin kwaryar birnin na yankin karamar hukumar birni da kewaye ne da ake kira AMAC. AMAC na da gundumomi 14 da suka hada Maitama, Asokoro, Garki, Wuse da kwaryar Abuja da ake kira Central Business District.
Sauran sun hada da Kado, Durumi, Gudu, Utako, Jabi, Mabushi, Katampe, Wuye da Gwarimpa.
Sabanin sauran kananan hukumonin guda biyar, birnin Abuja na da nasa matsalar tsaron daban da ake kira 'One Chance' da Turanci, inda wasu masu motar haya ke daukar mutane da sunanfasinja amma sai su buge da yi musu fashi ko kuma garkuwa.
Wani mazaunin birnin Abuja ya shaida wa BBC cewa " rannan a Zone 4 na ga yadda 'yan sanda suka kama wasu mutane da suka sato wata mace a bayan motarsu."
Baya ga 'One Chance' a kwai ayyukan bata-gari nan da can a birnin na Abuja kmar kwace da fashi da makami da sata.
Rundunar 'yan sandan birnin tarayya ta ce duk tana sane da irin wadannan muggan ayyuka da ke faruwa a Abuja da kewaye kuma tana yin iya yinta wajen ganin bata-garin ba su samu wuri a birnin ba.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Josephine Adeh ta ce "yanzu mun sake sabon tsari inda muka baza 'yansandanmu a lungu da sakon Abuja domin kama barayi da masu yin one chance da 'yan iskar gari da ma masu satar motocin jama'a."
Dangane da garkuwa da mutanen a sauran kananan hukumomin na waje, Josephine ta ce "muna nan mun dana musu tarko kuma da iznin Allah mun fi karfinsu saboda ba za mu bari a mayar da birnin tarayya tuwon tushe ba. Muna aiki tare da rundunar jami'an DSS da sauran jami'an tsaro."
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Shin ko birnin tarayya Abuja na fuskantar matsalar tsaro? – BBC
