Global site navigation
Na gargajiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, a filin jirgin sama.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan siyasar sun hadu ne a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da mai magana da yawun Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X.
Kara karanta wannan
Kungiyar Kiristocin Najeriya ta dare gida 2, an samu hatsaniya kan Seyi Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso da Barau, duk ’yan jihar Kano ne, sai dai suna jam’iyyun siyasa mabambanta, domin Barau na jam’iyyar APC ne, yayin da Kwankwaso ke jagorantar NNPP.
Yanzu Sanatan na Arewacin Kano shi ne shugaban majalisar dattawa, Kwankwaso ya taba zama mataimakin shugaban majalisar wakilai a 1992.
Wasu hotuna da suka bayyana sun nuna lokacin da su biyun ke musabaha cikin girmamawa da dariya, alamar mutunta juna da nuna hadin kai duk da sabanin siyasa.
A wani labari na daban Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, Kano, ta bayyana shirin ta na ba Sanata Kwankwaso digirin girmamawa na digirgir.
Karramawar, a cewar jami’ar, na zuwa ne a matsayin girmamawa bisa yadda Kwankwaso ya assasa jami’ar a lokacin da yake gwamnan Kano, da kuma yadda ya fifita ilimi a ayyukansa.
Kwankwaso ya kasance daya daga cikin fitattun shugabannin da suka sadaukar da kansu wajen farfado da ilimi da bai wa matasa damar karatu.
Kara karanta wannan
Sabon shugaban NNPCL ya ci gaba da fatattaka, ya kori shugabannin matatun mai 3
Jami’ar ta bayyana cewa ya dace a karrama Kwankwaso saboda gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa makarantar da tallafawa dalibai a lokacin gwamnatinsa ta shekarar 2011 zuwa 2015.
Hon. Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook cewa jami’ar ta ce:
Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu, suka roki Allah SWT ya kara masa lafiya da karin nasarori a rayuwa da shugabanci.
Ana sa ran bikin karramawar zai samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan.
A wani rahoton, kun ji cewa Dr Abdullahi Baffa Bichi ya zargi gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da yin ba daidai ba a gwamnatinsa cikin shekara biyu.
Kara karanta wannan
2027: Daliban Arewa daga jihohi 19 sun gana da Atiku Abubakar a Abuja
Dr Baffa Bichi ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi badakala mai tarin yawa cikin shekara biyu da ta zarce matsalolin da aka samu a lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje.
Bichi ya fito da maganganun ne watanni bayan sallamar shi daga matsayin sakataren gwamnatin Kano da Abba Kabir Yusuf ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng
Mun zaba maka wannan
Duba karin labarai a nan
Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Hadu da Sanata Barau Jibrin a Abuja – Legit.ng
