Masana sha'anin tsaro sun ce harin da ake zargin an kai wa jirgin ƙasa da ke jigilar fasinja daga Abuja zuwa Kaduna ya ƙara fito da girman matsalar tsaro a Najeriya.
Fasinjojin da abin ya rutsa da su, sun ce sun ji wata babbar kara ta fashewar wani abu, wadda ta yi sanadin tsayawar jirgin cik, inda ake zargin hari ne aka kai wa jirage biyu da ke jigila daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Laraba da dare da kuma safiyar Alhamis.
Duk da yake gwamnatin Najeriya ba ta ayyana wadanda take zargi ba kawo yanzu kuma babu wata kungiyar da ta fito ta yi ikirarin kai harin, amma masanan tsaro na ganin ƴan bindiga ne da suka addabi arewecin Najeriya.
Masana na dora alhakin aukuwar hakan kan hare-haren 'yan bindiga, amma hukumar jiragen kasan ta dora laifin ne kan masu yi wa hanyar jirgin ta'adi.
Malam Kabiru Adamu, masanin tsaro a Najeriya kuma shugaba kamfanin Beacon Consulting ya ce ɓangaren ƴan bindiga biyu za su iya kai harin – ɓangaren ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane da kuma ƙungiyoyar Iswap mai da'awar jihadi a arewa maso gabas.
Masanin kuma ya ce wasu bayanai sun nuna cewa ƙungiyar Ansaru ta samu sansani a yankin, kuma ba za a cire ta daga tunanin kai harin ba.
Sai dai kuma Barista Audu Bulama Bukarti, babban mai sharhi kan harkokin 'yan tayar da kayar baya da ke cibiyar Tony Blair ta Landan ya ce yana da wahala a ce Ansaru ce ta kai harin saboda da'awar da ta ke cewa ba sa kashe mutane.
"Ansaru ba ta fiye kai hare hare ba tun da mayaƙan suka ɓalle daga Boko Haram. Ƴan fashin daji ne suka kai wannan hari kan jirgin ƙasa," in ji Bukarti.
Ya ce bayanai na nuna cewa ƴan bindiga ne na jihar Zamfara bayan da ake fatakkesu suka dawo yankin Rijana a Kaduna.
Masanan sun ce bisa bayanan da suka fito da nazarin da suka yi – wadanda suka kai harin sun kai ne da niyyar jirgin ya tsaya a inda suka kai harin.
Amma ba a san manufar kai harin ba, idan da jirgin ya tsaya. Masanin tsaro Malam Kabiru ya ce hasashensu na nuna cewa an kai harin ne da niyyar sace wadanda ke cikin jirgin.
Har yanzu hukumomi ba su bayyana bincikensu abin da ya gano ba kan manufar kai harin.
Asalin hoton, OTHERS
Masanan sun ce hari kan jirgin ƙasa mummunan al'amari ne da kuma barazana ga matsalar tsaron Najeriya.
Kuma hari ne da zai ƙara dagula lamurran sufuri da kasuwanci da aikin gwamnati a jihohin arewa da Abuja.
Masanan sun ce mafita kawai a yaƙi ƴan bindigar a hanyoyin da ake yakar yan ta'adda.
"Ya kamata a shiga a kama su ko a kashe su, domin barinsu har su samu damar dasa nakiya babbar barazana ce," in ji Malam Kabiru
Ya ƙara da cewa ya kamata a gina ganuwa a titin jirgin domin duk wanda zai ratso titin an san da shi.
Ya kuma ce akwai buƙatar a sanya na'ura da za ta dinga sa ido wacce za ta bayar da damar ganin duk wanda ya ratsa ko ƙoƙarin yin ɓarna a titin jirgin.
Sannan a cewar masanin akwai buƙatar yin tsari na inganta jami'an tsaro ta yadda za su dinga zuwa wurare cikin dan karamin lokaci.
Masu bin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja, babban birnin Najeriya sun yi tsokaci kan matakin hukumar sufurin ƙasar na dakatar da jigilar fasinjoji har illa masha Allahu.
Wani fasinja da ke bin jirgin ƙasan ya shaida wa BBC cewa dakatar da jigilar jiragen kasan a yanzu ta sa dole zai rage yawan tafiye-tafiyen da yake yi zuwa Kaduna daga Abuja, domin kare kansa daga abin da ka je ya zo.
"Dama tsoron yanayin da hanya ke ciki ne ke sa mu ajiye motocinmu mu bi jirgin kasa, amma yanzu ga shi ma bai tsira ba, yanzu haka na so in je Kaduna amma saboda rashin hanya na zauna a gida na haƙura," in ji shi.
A cewarsa, "Idan ba a samu hanyar jirgin ba nan kusa, dole haka zan kama hanya na bi mota, amma fa za mu hau hanya ne saboda shahada kawai, kuma rashin natsuwa da halin tsaron nan ne yake samu kullum zama cikin taraddadi.
Ya ce tun lokacin da aka samu wannan matsala bai fita daga Abuja ba, yana nan zaune wuri guda domin kare kansa daga fadawa irin wannan matsala.
Asalin hoton, OHERS
"Ina cikin Abuja, saboda idan ka fita ba ka san inda za ka fada ba, ni nasan wanda masu garkuwa da mutanen nan suka kama, halin da ya shiga babu daɗin ji ko kadan, dole mutum ya kiyaye kansa," in ji wannan matafiyi da ya saba bin titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna".
Shi kuwa wani fasinjan cewa ya yi dama dalili biyu ne ke sa mutane suna bin jirgin ƙasan, na farko sauƙi, na biyu kuma halin da ake ciki na tsaro, mutane na ganin kamar za su fi zama lafiya, amma yanzu dole kowa zai shiga firgici.
A cewarsa "Ya zama wajibi gwamnati ta duba abin da za ta yi kan bangaren tsaro domin su kadai ne dama wadannan hanyoyi guda biyu, kuma ba kowa ne ke da kudin da zai biya ya hau jirgin sama ba."
Shi ma wannan matafiyin ya ce dole idan ta kama haka zai bi titin mota ya yi tafiya, tun da babu yadda za a yi.
Mutane da dama dai suna bin jirgin ne daga babban birnin Najeriyar saboda yawan hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa kan motoci da ke zirga-zirga kan titi, da kuma sace mutane don neman a biya kudin fansa.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Su wa suka kai wa jirgin kasa hari daga Kaduna zuwa Abuja? – BBC
