Asalin hoton, Others
Gwamnatin Najeriya ta sake bayar da kwangilar gyaran babban titin Abuja zuwa Kaduna ga wasu kamfanoni uku bayan karɓe aikin daga kamfanin Julius Berger.
Ministocin ayukka da watsa labarai na ƙasar ne suka sanar da hakan yayin ƙaddamar da sake aikin gyaran hanyar a ranar Alhamis a garin Tafa da ke jihar Naija.
Yanzu dai an ɗebawa kamfanonin watanni 14 su kammala aikin kamar yadda ministan yaɗa labarai na Najeriya, Alhaji Muhammad Idris ya shaida wa BBC.
"Wannan hanya dai da ake ginawa daga Kano zuwa Abuja wani abu ne da ya damu mutane musamman mutanen arewacin Najeriya…Shugaba Tinubu ya ce a tabbatar an yi duk abin da za a yi domin kammala aikin wannan hanya." In ji Muhammad Idris.
Ya ƙara da cewa kamfanin Julius Berger ne suka yi ta janƙafa wani abu da ya sa ahar aka soke kwangilar.
Ministan ya kuma ce yanzu an ba wa kamfanoni guda huɗu da za su tabbatar da kammala aikin a watanni 14.
"Shugaba Tinubu ya ce dole ne a tabbatar an kammala wannan aiki domin jama'a su fita daga ƙangin wahalar da suke ciki sakamakon rashin kyawun wannan hanya. Yanzu kamfanonin za su sake shimfiɗa sabuwar hanya mai ɗauke da kwalta da kankare irin waɗanda ake yi a kudancin Najeriya." In ji minista.
Ministan ya kuma ƙara da cewa yanzu a sabuwar yarjejeniyar za ta ƙunshi ƙarin kilomita 10 a ƙarshen titin wato birnin Kano, inda titin zai kai har zuwa filin jirgin Malam Aminu kano da ke birnin na Kano. Haka kuma za a shimfiɗa ƙarin kilomita 10 daga Abuja inda za a haɗa titin da na tafiya Lokoja.
A shekarar 2018 ne dai gwamnatin shugaba Muhammad Buhari ta ƙaddamar da fara aikin titin mai tsawon kilomita 431.
Kuma a lokacin ƙaddamarwar, ministan lantarki da ayyuka da gidaje na lokacin Babatunde Raji Fashola ya ce za a kammala titin ne a shekaru bakwai.
"Nan da shekarar 2022 ne za a kammala hanyar da ke tsakanin Kaduna da Zaria, wanda wannan babban cigaba ne.
"A 2023 za a kammala hanyar da ta tashi daga Kaduna ta dangane ga Kano, sai kuma a 2025 za a kammala hanyar Abuja zuwa Kano baki ɗayanta," in ji Fashola.
Ministan ya kuma ce an ware kuɗaɗe da suka kai naira biliyan 155 domin aiwatar da aikin.
Rashin baiwa kamfanoni masu aiki a hanyar kuɗaɗe da rashawa da cin hanci da kuma faɗuwar darajar naira sun sanya aikin na ta jan ƙafa.
Mafi yawancin direbobin da ke bin hanyar sun shaida wa BBC cewa a kowane lokaci suna tafiya a kan titin ne cikin fusata da ɓacin rai saboda rashin tabbas ɗin da suke fuskanta wurin isa inda suka nufa a kan lokaci.
Abdul Ɗan Fulani, wan direba ne da ya bayyana mamakinsa kan yadda aka gaza kammala aikin titin duk da dogon lokacin da aka ɗauka ana aikin, ''gaskiya muna shan wahala, don wani lokaci idan hanyar ta cunkushe sai ka ga har kwana ake yi a kan hanya, wannan lamari yakan janyo asarar dukiya har ma da rayuka a wasu lokutan.'' In ji shi.
Ya ƙara da cewa matsalar rashin tsaro na ƙara ta'azzara halin da su ke shiga sakamakon fargabar da suke yi ta cin karo da ƴan bindiga da za su iya kai masu hari a kowane lokaci.
Ya ce: ''Muna fama da matsalar satar mutane, don ko a wannan makon da ƙyar na sha domin na ɗauko mutane na biyo kan wannan titin na zo na tarar da ƴan fashin daji sun fito sun tare hanya, Allah ne kawai Ya kuɓutar da ni. A ƙarshe ma dai a hanya na kwana.''
Wasu daga cikin direbobin sun kuma koka kan yadda lalacewar titin ke jawo masu asara domin kuɗaden da suke kashewa kan gyaran ababen hawansu kamar yadda Bashir Musa wani direban motar ɗaukar kaya ya bayyana: ''Duk lokacin da muka bi wannan hanyar sai mun yi gyararraki a motocinmu domin irin ramukan da suke kan titin, mu kaɗai muka san irin wahalar da muke sha a kan wannan titin.''
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
'Tinubu ya ba da umarnin kammala titin Abuja zuwa Kano a watanni 14' – BBC
