Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya koma Najeriya bayan da ya kai ziyarar aiki zuwa Faransa da Birtaniya.
Shugaba Tinubu ya samu tarba daga manyan muƙarraban gwamnatinsa a lokacin da jirginsa ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, da ke Abuja, ranar Litinin da daddare.
Ɗaya daga cikin masu magana da yawun SShugaban Najeriyar, Dada Olusegun ya tabbatar da hakan a shafinsa na X inda ya ce "Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja bayan ziyarar da ya kai Paris da birnin London."
Wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin da suka yi wa Shugaba Tinubu maraba sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume da Shugaban ma'aikata a fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
A ranar 2 ga watan Afirilu, 2025, Shugaba Tinubu ya yi bulaguro zuwa Paris, babban birnin Faransa inda daga can ya riƙa tafiyar da al'amuran mulki.
Sai dai wasu yan Najeriya sun soki matakin inda suke ganin kamata ya yi ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima.
Tafiyar ta Shugaba Tinubu ta kuma janyo suka daga manyan ƴan adawa a Najeriya – Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Jam'iyyar Labour inda suke ganin bai kamata a ce shugaban ƙasar ya kaɗa kai ya fice daga ƙasar ba a daidai lokacin da ake ƙara fuskantar matsalar tsaro a ƙasar.
Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta mayar da martani tana karyata raɗe-raɗin cewa Shugaba Tinubu ya tafi neman lafiyarsa ne.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Tinubu ya koma Najeriya bayan 'ziyarar aiki' a Paris da London – BBC
