Tirelar siminti ta Dangote ta haddasa gobara a Abuja, motoci 14 sun ƙone – TRT Global

Aƙalla mutum shida suka rasu bayan wata tirelar Dangote ɗauke da siminti ta faɗi sannan ta kama da wuta a Nijeriya.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a kan hanyar Abuja zuwa Keffi bayan tirelar ta ƙwace wa direban inda ta afka wa motoci 14 waɗanda suka maƙale a cikin cunkoson ababen hawa, kamar yadda ‘yan sanda a Abuja babban birnin ƙasar suka bayyana.
A wata sanarwa da ‘yan sandan ƙasar suka fitar, sun bayyana cewa an zaƙule mutum shida daga wurin da lamarin ya faru inda aka garzaya da su asibiti amma likitoci suka tabbatar sun rasu.
Lamarin ya jawo cunkoson ababen hawa a kan hanyar ta Karu, wadda muhimmiyar hanya ce ta tashi daga Abuja zuwa Nasarawa.
Sai dai a sanarwar ta ‘yan sandan, tuni jami’an kashe gobara da sauran jami’an tsaro da al’ummar gari suka taimaka wurin kashe gobarar da kuma sauƙaƙa cunkoson ababen hawan.
Sakamakon rashin ingantacciyar hanyar sufurin jirigin ƙasa, ana yawan samun hatsarin manyan motocin ɗaukar kaya da ɗaukar mai a Nijeriya, wadda ita ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan jama’a a Afirka.
Ko a Janairun bana sai da mutum 98 suka rasu sakamakon fashewar wata tankar mai a Jihar Neja da ke arewacin Nijeriya bayan wata tankar ta yi hatsari inda wasu suka je kwalfar man fetur.
 

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds