Tsohon ministan Abuja, Jeremiah Useni ya rasu – BBC

Asalin hoton, Others
Tsohon ministan birnin tarayyar Najeriya Abuja, Jeremiah Useni ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.
Jeremiah Useni ya rasu ne a ranar Alhamis 23 ga watan Janairun 2025 bayan fama da rashin lafiya.
An haifi shi ne a ranar 16 Fabareru, a shekara ta 1943, a garin Lantang, da ke yankin kudancin Jihar Filato.
Gwamnan Jihar Fulato, Caleb Muftwang ne ya sanar da mutuwar marigayin, kamar yadda sanarwar da sakataren yada labaran gwamana ya fita a ranar Alhamis.
Gwamna Muftwang ya bayyana mutuwar Useni a mastayin babban rashi ba ga iyalansa, da rundunar sojin Najeriya, da jihar Fulato kaɗai ba, sai dai ga ilahirin Najeriya baki daya.
Jeremiah Useni ya kai matakin Laftanar-Janar a aikin soja, sannan ya taɓa zama Ministan harkokin Sufuri da na babban birnin Najeriya Abuja, a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya na soji marigayi Sani Abacha, da Quarter Master na rundunar sojin Najeriya.
An kuma taɓa naɗa shi shugaban wakilan ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Najeriya ta ACF, da suka gana da gwamnonin jihohin arewacin kasar, da sauran shugabanin yankin don samar da manufa guda ɗaya da nufin ci gaban yankin.
Bayan ya bar aikin soja, Janar Useni ya shiga siyasa, inda ya tsaya takarar gwamnan jihar Filato ƙarƙashin jam'iyyar PDP a zaɓen 2019.
Ya kuma taɓa zama mataimakin shugaban tsohuwar jam'iyyar ANPP, sannan ya zama sanata mai wakilatar Filato ta kudu a 2015, a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.
Har ila yau ya taɓa zama gwamna a tsohuwar jihar Bendel a shekarar 1984.
Ba za a manta da marigayi Jeremiah Useni ba saboda yadda aka rinƙa yada jita-jitar cewar shi ne zai gaji marigayi tsohon shugban Najeriya Sani Abacha, bayan rasuwarsa saboda kusancin sa da shi.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds