Waiwaye: Kisa a hanyar Abuja, umarnin Buhari na fatattakar ƴan bindiga, cire tallafin fetur – BBC

Kamar kowane mako, a yau ma mun yi waiwaiye kan muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata tun daga Lahadi 21 ga watan Nuwambar 2021 zuwa Asabar 27 ga wata.
Ƴan bindiga sun kashe tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara
Asalin hoton, FACEBOOK
A ranar Lahadin da ta gabata ne ƴan bindiga suka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.
Bayanai sun ce an samu asarar rayuka ciki har da wani tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.
'Yan uwan marigayin sun tabbatar wa BBC Hausa faruwar al'amarin kuma sun ce ya gamu da ajalinsa ne lokacin da 'yan bindigar suka tare hanya.
Malam Mohammed Sirajo Hamidu ƙanin marigayin ne kuma ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun buɗe wuta ne lokacin da direban yayansa ya yi ƙoƙarin juyawa domin komawa Kaduna bayan da suka fahimci cewa sun faɗa tarkon masu garkuwa da mutane.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin fatattakar ƴan bindigar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma na wasu sassan ƙasar.
Jaridar Daily Trust a Najeriyar ta ruwaito ministan harkokin cikin gida na ƙasar Rauf Aregbesola yana sanar da hakan a yau Alhamis bayan taron majalisar tsaro ta tarayya wanda shugaban ƙasar ya jagoranta a fadarsa.
Ya bayyana cewa shugaban ya ba dukkannin jami'an tsaron ƙasar umarni da kada su yi ƙasa a gwiwa su tabbatar sun kawar da duk wasu ɓarayi da masu garkuwa da mutane da duk wasu nau'uka na laifuka.
Asalin hoton, HQ NIGERIAN ARMY/FACEBOOK
A makon da ya gabata ne Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ɓarayin daji masu kai hare-hare da satar mutane 128 a arewa maso yammaci da kuma da ƴan Boko Haram 140 a arewa maso gabashin ƙasar.
Rundunar sojin ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Bernard Onyeuko ya fitar inda ya bayyana irin nasarorin da ayyukan rundunonin sojin suka samu a sassan Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.
Rundunar ta ce alƙalumman sun shafi ayyukan rundunoninta na tsawon mako biyu daga ranar 11 ga Nuwamba zuwa 25 ga watan.
Sanarwar ta ce an yi wa sansanonin ƴan bindiga da ƴan Boko Haram ruwan wuta da kama wasu daga cikinsu.
Asalin hoton, Getty Images
A makon da ya gabata ne yan Najeriya da dama suka fusata game da shirin da gwamnatin kasar take yi na janye tallafin man fetur baki daya daga shekara mai zuwa.
Hakan ya sa Shugaban kamfanin man fetur na kasar, Mele Kyari, ya ce idan aka cire tallafin za a iya sayar da man fetur ɗin tsakanin 320 zuwa 340.
A shafukan sada zumunta musamman Facebook, kusan duk inda mutum ya leƙa zancen ake yi inda akasari ake ta Allah-wadai da lamarin.
Akasari mutane suna watsi da wannan lamarin ne saboda kuka da suke yi na tsadar rayuwa musamman hauhawar farashin kayayyakin abinci da kuma rashin tsaro da ake fama da shi.
Asalin hoton, Getty Images
A makon da ya gabata ne Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta caccaki kasar Amurka kan cire Najeriya daga cikin jerin masu tauye ƴancin addinai a ƙasar a shekarar 2021, tana mai cewa ce har yanzu kungiyoyin 'yan ta'adda da sauran kungiyoyin addinin musulunci na ci gaba da muzguna wa Kiristoci a kasar.
Uwar kungiyar kiristocin ta ce bayanai ko kididdiga da gwamnatin Amurka ta yi amfani da su wajen fitar da Najeriya daga cikin jerin ƙasashen da ake fuskantar wannan matsala musamman kan batun 'yancin addini ya bata mamaki.
A ranar Laraba sakataren harkokin wajan Amurka, Anthony Blinken ya fitar da wata sanarwa da ta bayanna Rasha da China da wasu kasashe takwas a matsayin masu keta hakkin adini, kuma ba bu sunan Najeriya a ciki wadda a shekarar 2020 tana cikin jerin kasashe da ake zargi suna musguna wa sauran addinai .
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds