A lokuta da dama musamman lokacin damina a kan samu matsanancin cunkoson ababen hawa a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ke nema ya zama ruwan dare kan wannan hanyar da ke da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin Najeriya.
An bayar da kwangilar yi wa wannan titin kwaskwarima ne a shekara ta 2018 kan kuɗi Naira biliyan 155, sai dai bayan gano irin matuƙar lalacewar da titin ya yi aka sauya kawangilar daga kwaskwarima zuwa sabon titi.
Mafi yawancin direbobin da ke bin hanyar sun shaida wa BBC cewa a kowane lokaci suna tafiya a kan titin ne cikin fusata da ɓacin rai saboda rashin tabbas ɗin da suke fuskanta wurin isa inda suka nufa a kan lokaci.
Abdul Ɗan Fulani, wan direba ne da ya bayyana mamakinsa kan yadda aka gaza kammala aikin titin duk da dogon lokacin da aka ɗauka ana aikin, ''gaskiya muna shan wahala, don wani lokaci idan hanyar ta cunkushe sai ka ga har kwana ake yi a kan hanya, wannan lamari yakan janyo asarar dukiya har ma da rayuka a wasu lokutan.'' In ji shi
Ya ƙara da cewa matsalar rashin tsaro na ƙara ta'azzara halin da su ke shiga sakamakon fargabar da suke yi ta cin karo da ƴan bindiga da za su iya kai masu hari a kowane lokaci.
Ya ce: ''Muna fama da matsalar satar mutane, don ko a wannan makon da ƙyar na sha domin na ɗauko mutane na biyo kan wannan titin na zo na tarar da ƴan fashin daji sun fito sun tare hanya, Allah ne kawai Ya kuɓutar da ni. A ƙarshe ma dai a hanya na kwana.''
Wasu daga cikin direbobin sun kuma koka kan yadda lalacewar titin ke jawo masu asara domin kuɗaden da suke kashewa kan gyaran ababen hawansu kamar yadda Bashir Musa wani direban motar ɗaukar kaya ya bayyana: ''Duk lokacin da muka bi wannan hanyar sai mun yi gyararraki a motocinmu domin irin ramukan da suke kan titin, mu kaɗai muka san irin wahalar da muke sha a kan wannan titin.''
Direbobin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta ɗaukar matakan tabbatar da an gaggauta kammala aikin titin domin su sami sauƙin gudanar da al'amuransu.
Rahotanni dai na cewa kamfanin da aka bai wa kwangilar aiki ya kwashe kayan aikinsa, wanda hukumomi suka bayyana cewa babban kuskure aka yi tun farko na bai wa kamfani shi ɗaya aikin gyaran wannan titin.
Dr Yakubu Adam Ƙofarmata shi ne babban sakataren ma'aikatar ayyuka ta Najeriya kuma ya bayyana wa BBC cewa bisa la'akari da muhimmancin titin gwamnati ta yi nazarin sauya salon aikin baki ɗaya.
Ya ce: kamfanin na guɗa ɗaya ya kasance sai yadda ya yi da mu, domin yanzu kuɗin aikin ya ninka yadda aka bayar da shi a shekarun baya, kullum kamfanin cewa yake yi a ƙara masa kuɗi, kuma gwamnati ba ta da kuɗin da za a yi hakan. Da an ce bai kamata a ƙara ba sai kawai su kwashe kayayyakinsu.''
Sai dai Dr Yakubu ya bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba aiki zai kankama a titin, ''Muna sa ran cewa nan da wata shida zuwa takwas za a yi ƙoƙarin tabbatar da an gama titin nan.'' In ji shi.
A farkon wannan shekarar ta 2024 Ministan ayyuka Dave Umahi, ya sanar da bai wa kamfanin da ke aiki Naira biliyan 13 domin ci gaba da aiki. Gwamnati ta kuma sanar da ware Naira biliyan 33 na ko-ta-kwana domin tabbatar da aikin ya kammala.
A watan Agustan da ya gabata gwamnatin Najeriya ta cimma matsaya da wakilan kamfanin cewa za a riƙa ba su Naira biliyan 20 a kowane wata domin gaggauta ƙarasa aikin titin cikin watanni 14 masu zuwa.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Yadda aikin titin Abuja zuwa Kaduna ya ƙi ci ya ƙi cinyewa – BBC
