Yadda rikici tsakanin 'yansandan da 'yan shi'a ya jawo hasarar rayuka a Abuja – BBC

Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce ta kama mabiya mazhabar shi’a da dama, bayan kisan jami’anta biyu yayin wata arangama a Abuja, babban birnin kasar.
Lamarin ya faru ne, lokacin da ‘yan shi’ar ke tattakin yaumul arba’in, da suke gudanarwa kowacce shekara.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Najeriya a birnin Abuja, SP Josephine Adeh ta ce jami'anta na tsaka da aikinsu a wani wurin bincike da ke kusa da kasuwar Wuse ‘yan kungiyar ta IMN suka far musu.
"Yaran mu su na aiki, sai ga shi sun fito, mata a gaba da yara, mazan na ta baya, kawai kafin a ankara mai yake faruwa su ka fara jifa da bam din da suka yi da kwalba."
"Ba abin da mu ka yi musu, kawai suka fara kai wa jami’an mu hari, suka kashemu na ‘yansanda guda biyu tare da raunata wasu uku sannan sun kona motocci guda uku," in ji SP Adeh.
Rundunar ‘yansanda Najeriya ta ce su na kan gudanar bincike a kan abin da ya haifar da yamutsin.
"Mun kama wasu ‘yan shi’a a lokacin kuma muna kan bincike domin mu san abinda ya haifar da yamutsin. Ba bu wani da aka kashe daga bangaren ‘yan shi’ar,"in ji ta.
Kwamishinan 'yansandan birnin na Abuja, CP Benneth C. Igweh ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu.
Sai dai daya daga cikin jagororin kungiyar ta IMN, Malam Abdullahi Muhammad Musa ya ce ba haka abin ya wakana ba.
Ya ce tun ranar Juma’a suka fitar da sanarwar a kan cewa za su fito su yi tattaki kamar yadda suka saba duk shekara.
"Lafiya lau muka zo Wuse 2, mu na zuwa kasuwar Wuse ‘yansanda su ka bude mu na wuta, wasu su ka yi gaba da tattakin, har mu ka je Berger su ma ‘yansandan da ke Berger su ka harba ma na hayaki mai sa hawaye, sun harbi mutane da dama, a gaba na wani ya mutu".
Ya yi ikirarin cewa ‘yan sandan sun harbi mutane da dama tare da musanta zargin cewa suna rike da makamai kuma sun tare wuri.
"Ba mu taba tare wa kowa hanya ba , Su dai kawai sun bude ma na wuta , ba yau su ka saba kashe mana mutane ba,’’ in ji Malam Abdullahi
A Najeriya dai rashin jituwa tsakanin jamian tsaro da mabiya mazhabar shia ba wani sabon abu bane.
Mafi muni ita ce ta shekarar 2015 lokacinda aka kashe daruruwan 'yan kungiyar da jami'an tsaro su ka zarga da farwa shugaban sojojin kasar na wancan lokaci yayin da ayarin motocinsa ke kokarin wucewa a garin Zaria.
A shekarar 2019 kotu ta haramta kungiyar ta IMN kan zargin ta'adanci da kuma tayar da zaune tsaye.
Sai dai zargi ne da ta musanta.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds