Asalin hoton, NRC
'Yan bindigar da suka kai hari tare da sace fasinjoji a jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja sun sako wasu daga cikinsu ranar Asabar.
Mutum 11 'yan fashin suka sako saɓanin alƙawarin da suka yi tun farko cewa za su sako dukkan matan da suke tsare da su, kamar yadda mawallafin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu ya ruwaito.
Tukur wanda shi ne mai shiga tsakanin 'yan bindigar da kuma gwamnatin Najeriya, ya ce mata shida ne da kuma maza biyar aka sako a yanzu bayan shafe tsawon loƙaci ana tattaunawa.
Ɗaya daga cikin 'yan uwan waɗanda aka sako ya tabbatar wa BBC Hausa da sakin ɗan uwan nasu.
A ranar Litinin, 28 ga watan Maris 'yan bindigar ɗauke da makamai suka kai wa jirgin ƙasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna hari, inda suka kashe mutum bakwai, suka raunata wasu da dama sannan suka sace wasu.
Gwamnatin Najeriya ta ce mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne masu iƙirarin jihadi suka kai harin tare da haɗin gwiwar wani gungu na 'yan fashin daji.
Wasu majiyoyi sun shaida wa mai shiga tsakanin cewa 'yan bindigar sun rage yawan adadin mutanen da suka ce za su sako ne saboda buƙatar da gwamnatin Najeriya ta gabatar musu, inda su kuma suka kafa nasu sharaɗin.
"Mazan cikinsu an sake su ne saboda rashin lafiya da suke fama da ita, a cewar wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta," kamar yadda jaridar Desert Herald ta bayyana. "Su kuma matan suna cikin waɗanda da ma aka yi yarjejeniya tun farko, in ji rahoton.
"Tun farko an amince cewa za su sako dukkan matan da ke hannunsu yayin da ake ci gaba da sasantawa kan sauran mutanen, amma sai suka rage adadin mutanen da za su saka ɗin saboda gwamnati ta buƙaci a haɗo da duka waɗanda ke fuskantar matsananciyar rashin lafiya ko rauni.
"Masu garkuwar sun kafa sharaɗin cewa za su saki mutanen ne kawai idan gwamnati ta sako 'ya'yansu matasa (da ba su kai shekara 20 ba) da jami'an tsaro suka kama."
Rahoton ya ƙara da cewa mai shiga tsakanin ya faɗa wa masu garkuwar cewa gwamnati ba za ta yarda da haka ba sannan kuma sai sun saki wasu daga cikin mutanen da ke hanunsu.
Sai dai Malam Tukur Mamu bai bayyana ko gwamnati ta saki 'ya'yan nasu ba.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
'Yan bindiga sun sako wasu daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa na Abuja-Kaduna – BBC
