Global site navigation
Na gargajiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja – Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ofishinta a Abuja.
Rundunar ya gayyaci basaraken ne domin amsa tambayoyi kan rikicin bikin Sallah da ya faru a jihar Kano.
Rahoton Leadership ya bayyana cewa gayyatar ta biyo bayan rikicin da ya faru a ranar Sallah, lokacin da tawagar Sarkin ke komawa daga filin Sallah zuwa fada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani dan sa-kai mai suna Surajo Rabiu ya rasa ransa a rikicin, yayin da wani mutum daya kuma ya jikkata, wanda hakan ya bata farin cikin bikin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun tashin hankali a Kano, bayan haramta gudanar da bikin sallah na bana saboda matsalar tsaro.
Sai dai duk da hana hawan, tawagar motocin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta ci gaba da gudanar da zagayen Sallah a rana ta uku.
Kwamishinan ‘yan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kafa kwamitin mutane takwas domin gudanar da bincike na musamman kan rikicin da ya faru.
Takardar gayyata, wadda aka rubuta ranar 4 ga Afrilun 2025, na dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ibitoye a madadin DIG na Abuja, Daily Post ta ruwaito.
Takardar ta bayyana cewa:
An bukaci Sarkin ya bayyana gaban Sashen Bincike na Abuja, dake gaban Hedkwatar ‘Yan Sanda, Area 11, Abuja, da karfe 10:00 na safe, ranar Talata 8.
A lokacin hada wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, dangane da gayyatar da ‘yan sanda suka aikowa ba.
A baya, kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan ci gaba da yake zuba wa a jihar.
Sarki Sanusi II ya ce ƙoƙarin da gwamnan ke yi na inganta harkokin ilimi, kiwon lafiya noma da tsaro a jihar Kano ya cancanci a jinjina masa.
Gwamna Abba Kabir ya jaddada godiya ga mai martaba sarkin bisa jagorancin da yake yi da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami’ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.
Mun zaba maka wannan
Duba karin labarai a nan
Yan sanda sun gayyaci Sanusi II domin amsa tambayoyi kan rasa rai a bikin sallah – Legit.ng
