Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 115 a wurin zanga-zangar da 'yan Shi'a suka yi bayan da jami'anta suka yi arangama da su a Abuja, babban birnin kasar.
'Yan sandan sun kuma ce masu zanga-zangar sun lalata motocin jami'an tsaro tare da ji wa 'yan sanda 22 rauni.
Mabiya Shi'a, wandanda ke gangami domin neman a sako shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, sun ce 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye (Tear gas) wurin korarsu, sannan an harbi mambobinsu da dama.
Babu wata kafa mai zaman kanta da tabbatarwa da BBC ikirarin bangarorin biyu, amma wani wakilin BBC da ya ziyarci wurin ya ga gwangwanayen hayaki mai sa hawaye a warwatse.
Haka kuma rundunar 'yan sandan ta ce ta samu kayayyaki kamar su gwafa da rodi da duwatsu da kuma jajayen kyallayen da ake daurawa a ka.
End of Wanda aka fi karantawa
Ta kara da cewa za ta gurfanar da mutanen da ta kama a gaban kuliya bayan ta kammala bincike.
Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta kuma gargadi mabiya shi'ar da su daina tsare hanya a zanga-zangar tasu.
A ranar Litinin ne jami'an tsaro suka yi amfani da karfi wurin tarwatsa mabiya Shi'a da ke zanga-zangar da suka saba yi akai-akai a dandalin Unity Fountain da ke Abuja.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye (Tear gas) wurin korar masu gangamin.
Wakilin BBC da ya ziyarci wurin ya ga gwangwanayen hayaki mai sa hawaye a warwatse a wurin da lamarin ya faru.
Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a wasu shafukan sada zumunta sun nuna mabiya Shi'a suna jifan motar 'yan sanda wacce ita kuma ta rinka watsa musu ruwa.
Mabiya Shi'ar na wannan zanga-zangar ne a ci gaba da yunkurinsu na tilastwa gwamnati ta sako jagoransu na Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
Asalin hoton, Getty Images
Wani mabiyin Shi'a ya shaida wa BBC cewa an harbe shi tare da wasu 'yan Shi'ar da dama, sannan ya musanta cewa sun jefi jami'an 'yan sanda.
Ya kara da cewa jami'an tsaro sun yi awon-gaba da wasu daga cikin mabiyan nasu, sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar wa da BBC hakan.
Wannan lamari shi ne na baya-bayan nan a taho-mu-gamar da ake yi tsakanin jami'an tsaron da mabiya Shi'ar.
A ranar Juma'ar da ta gabata ma 'yan sanda sun kama wani mutum da suka bayyana a matsayin wanda yake shirya zanga-zangar da 'yan Shi'ar suka dade suna yi a dandalin Unity Fountain da ke Abujar.
Wani da ya shaida lamarin ya wallafa hotunan hargitsin a shafinsa na Twitter yana mai cewa: "Masu zanga-zanga da yawa na sake taruwa".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Babu karin bayanai
Sannan ya wallafa bidiyo yana mai cewa: "Hayaki mai sa hawaye da karar bindiga kawai ka ke ji".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Babu karin bayanai
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
'Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 115 a Abuja – BBC
