Asalin hoton, Nigeria Govt
Ministan makamashi da ayyuka da kuma gidaje na Najeriya Babatunde Fashola zai kaddamar da aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kano a ranar Talata.
Gwamnatin Najeriya ta ware kudi fiye da naira biliyan 155 domin aiwatar da aikin gyaran hanyar mai nisan kilomita fiye da 400.
A bara ne gwamnatin kasar ta amince da aikin bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka yi karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.
Hanyar dai ta dade da lalacewa al'amarin da kan janyo hadura motoci a wadansu lokuta tare da asarar rayuka.
Matafiya da sauran jama'a masu bin hanyar sun rika yin korafi a kan yadda hanyar ta lalace.
End of Wanda aka fi karantawa
A shekarar 2017 ne gwamnatin kasar ta gyara wani bangare na hanyar wato tsakanin Abuja zuwa Kaduna lokacin da aka rufe filin jirgin saman Abuja domin hanyar jirgi da za a gyara.
Sai dai daga bisani hanyar ta kara koma gidan jiya.
Asalin hoton, Nigeria govt
Asalin hoton, Nigeria govt
Asalin hoton, Nigeria govt
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Za a kaddamar da aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kano – BBC
