Turmutsutsun rabon tallafi ya kashe mutum 10 a Abuja – BBC

Asalin hoton, FCT Police Command
Aƙalla mutum 10 sun mutu, ciki har da ƙananan yara, yayin da da dama suka samu raunuku sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a cocin Catholic da ke unguwar Maitama a Abuja.
Lamarin ya faru ne ranar Asabar da safe lokacin da mutane suka yi dafifi a harabar cocin domin karɓar kayan tallafi da ta alƙawarta raba wa marasa ƙarfi da tsofaffi.
Cikin wata sanarwa da rundunar 'yansandan birnin Abuja ta fitar, ta ce cikin waɗanda suka mutu har da ƙananan yara huɗu, yayin da mutum takwas suka samu munanan raunuka, kuma suke karɓar magani a asibiti.
'Yansandan sun ce jami'an tsaro sun samu nasarar korar duka mutanen da suka taru a cocin waɗanda ta ce sun kai fiye da mutum 1,000.
Can ma a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin ƙasar rahotonni na cewa wasu mutane sun mutu bayan wani turmutsutsu da aka samu a wajen rabon tallafi a jihar a ranar ta Asabar.
Lamarin na zuwa ne kwanaki bayan wani turmutsutsun ya kashe ƙananan yara da 35 a birnin Ibadan na jihar Oyo, sakamakon wani bikin ƙarshen shekara.
Galibi dai dama a ƙarshen shekara masu hannu da shuni da ƙungiyoyin kan yi rabon tallafi musamman na kayan masarufi ga marasa ƙarfi, domin bukukuwan ƙarshen shekara.
Rundunar 'yansandan Abujan ta ce daga yanzu duk wanda zai yi irin wannan rabo na tallafi, dole ne ya sanar mata.
Domin ta samar da isassun jami'an tsaron da za su bayar da kariya a lokacin rabon.
Rundunar ta ce duk wanda ya ƙi bin wannan umarni to idan irin haka ta faru za a kama shi da laifin duk abin da ya faru.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

This will close in 0 seconds